Yadda kubewa ta ke kashe kwayoyin haihuwa
Binciken masana kiwon lafiya sun bayyana cewa akwai sinadarin da ke cikin kubewa wanda yake kashe kwayoyin haihuwa sai dai kuma sun bayyana wasu amfaninta ga jikin dan Adam
Wani babban jami'in harkokin bincike a Cibiyar bincike ta Oshodi a jihar Legas, Dr. Ochuko Erikainure, ya yi gargadin cewa kubewa wadda sunan ta na turanci 'OKRO' ta na gina jiki sosai sai dai kuma ta na iya kai wa zuwa rashin haihuwa a mazajen da su ka isa shekarun haihuwa .
Erikainure, wanda kwararre ne wajen sanin amfanin kayan itatuwa, ya kara da cewa kubewa ta na da wani nau'i na tasiri wajen rage karfin namiji ta fuskar jima'i.
Ya ce kubewa shuka ce wadda za ta iya girma a cikin yanayi na zafi da karancin ruwa kuma ta na da wani sinadari da ake kira Gossypol.
Sinadarin Gossypol ya na da tasiri wajen hana samuwar maniyyi a jikin dan Adam ta hanyar toshe wasu kwayoyin masu mahimmanci wajen karfafa samuwar maniyyi.
Wannan sinadari ya na kashewa maza kwayoyinsu na haihuwa kuma ya na rage samuwar maniyyi sosai a jikin namiji.
KU KARANTA: Yadda kayan lefe ke hana aure a kasar hausa
Sai dai kuma binciken ya nuna cewa akwai wani sinadarin Polyphenol da ya ke taimakawa wajen hana kamuwa da cututtuka kuma ya na rage maiko na jikin dan Adam da taimakawa wajen magance cutar daji wato Cancer.
Ya kara da cewa kubewa ta na da sinadaran gina jiki ma su amfani kwarai da gaske wanda yin amfani da kubewa ya na ba da kaso 20 cikin 100 da jikin dan Adam ya ke bukata a kowane yini na rana.
Binciken ya nuna cewa akwai wasu sinadari irinsu bitamin A, C da E da suke karawa fatar jikin mutum kyau da kuma ba da kariya ga masu ciwon sikari.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng