Kalli yadda Boko Haram ke rayuwa a cikin dajin Sambisa (Bidiyo)

Kalli yadda Boko Haram ke rayuwa a cikin dajin Sambisa (Bidiyo)

Kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo inda a ciki take nuna yadda suke rayuwa tare da fadin zata cigaba da yakar kasar Najeriya.

Bidiyon mai tsawon mintuna 29 ya nuna yadda yayan Boko Haram ke cinikayya a kasuwanni, yadda suke noma a ganakansu, da sauran al’amuran yau da kullum, kamar yadda Rediyo Najeriya ta ruwaito.

KU KARANTA: Saraki ya shawarci gwamnati ta fuskanci yaƙi da rashawa, ba wai ƙwato kuɗaɗen sata ba

Sai dai an kasa tantance wane tsagin Boko Haram ne ta fitar da wannan bidiyo, tun da dai ba’a ba shuwagabannin bangarorin biyu ba a ciki wato Abubakar Shekau da Abu Mus’ab Albarnawi.

Kalli yadda Boko Haram ke rayuwa a cikin dajin Sambisa (Bidiyo)
Yan Boko Haram

A cikin bidiyon an ga wani tsoho yana bayani cikin yaren Kanuri, inda yake masanta batun da Sojoji ke fadi na cewa sun kada Boko Haram: “Kuna ganin muna rayuwar mu cikin dadi, ku kalli gonakan mu masu albarka” Inji tsohon.

Haka zalika wani ma da yayi magana da Hausa yace “Zamu kare kasar mu ita bakin rai, ba zamu yarda kafirai su shigo mana yankin mu ba.”

Ga bidiyon kamar yadda majiyar Legit.ng ta kawo shi:

Idan ba’a manta ba , a yan kwanakin nan Al-Barnawi ya fitar da bidiyon sace wasu malama jami’an Maiduguri da suka sace a yayin da suke aikin binciken arzikin man fetur a yankin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli yadda Sojoji ke karkashe yan Boko Haram:

Asali: Legit.ng

Online view pixel