Jihar Bauchi ta tafka babbar asara: Baba Garba Gadi ya rasu

Jihar Bauchi ta tafka babbar asara: Baba Garba Gadi ya rasu

Tsohon gwamnan jihar Bauchi daya sha fama tare da gwamnan jihar na wannan lokaci Isa Yuguda, Garba Muhammad Gadi ya rasu a ranar Talata 1 ga watan Agusta.

Garba Gadi wanda shine Dan Buram na Katagum ya rasu ne a kasar Indiya inda yayi jinya sakamakon wata cuta data addabe shi wanda ba’a bayyana ba, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

KU KARANTA: Kalli hotunan katafariyar matatar mallakin hamshakin attajir Aliko Dangote

Legit.ng ta ruwaito Garba Gadi ya taba zama mataimakin gwamnan jihar Bauchi a shekarar 2007, bayan gwamna Isah Yuguda ya lashe zaben shekarar a karkashin jam’iyyar ANPP.

Jihar Bauchi ta tafka babbar asara: Baba Garba Gadi ya rasu
Garba Gadi

Sai dai ruwa yayi tsami tsakanin gwamna Isa Yuguda da Baba Gadi tun bayan da Isah Yuguda ya sauya sheka zuwa PDP bayan ya auri yarinyar shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, inda shi kuma Garba yaki binsa zuwa PDP.

Wannan mataki da mataimakin gwamnan Garba Gadi ya dauka ya sanya Isah Yuguda yunkurin tumbuke shi, amma sai Garban ya garzaya gaban kotu, wanda ta yanke hukuncin lallai sai an mayar da shi mukaminsa.

Daga bisani kuma Isah Yugudan yayi amfani da yan majalisun dokokin jihar inda yasa suka tumbuke Garba Gadi, yayin da shi kuma ya zabo Kaakakin majalisar Babayo Gamawa a matsayin sabon mataimakinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng