Boko Haram: Jami’an leken sirri na nazari a kan binciken kira da sakonnin wayar talho a yankin Magumeri

Boko Haram: Jami’an leken sirri na nazari a kan binciken kira da sakonnin wayar talho a yankin Magumeri

- Jami’an leken asiri na kasa na nazari a kan kira da kuma sakonnin wayar talho na mutanen da ke yankin Magumeri

- Jami’an tsaro na zargin mutanen yankin cewa zai yiwu suna ba da bayanai ga kungiyar Boko Haram

- Sace ma’aikatan jami’ar Maiduguri da wasu mutane zai iya kawo jinkiri ga wa’adin kama shugaban kungiyar Boko Haram

A cikin hare-hare na kwanan nan na ‘yan kungiyar Boko Haram wadda ta yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi da kuma sace-sacen mutane sakamakon aka yasa jami’an tsaro ta hadin leken asiri ke nazari a kan binciken kira da kuma saƙonnin wanyar talho na mazaunar yankin Yesu da ke Magumeri na Jihar Borno, kamar yadda rahoton PR Nigeria ta sanar.

Har ila yau majiyar ta bayyana cewa jami'an tsaro har da na leken asiri a cikin abubuwan da za su bincika za ta hada ko akwai wani alaka ko kuma hadin gwiwar tsakanin mazaunar hanyoyin yankin da aka yiwa jami’an tsaro da ma’aikatan kamfanin NNPC kwanton bauna tun da wannan hanyar ne ma’aikatan ke biyowa zuwa wuraren da suke binciken mai tun dama kafin wannan mumunar harin.

" Wannan kwanton bauna na 'yan ta'adda abin takaici ne kuma wani abin damuwa ne ganin yanda dakarun tsaro ke rakiya jerin gwanon ma’aikatan ko da yaushe da kuma bayar da cikakken tsaro a wannan hanyar, ba a ta ba samu wata damuwa ko irin wannan al’amarin ba”. A cewar majiyar.

Boko Haram: Jami’an leken sirri na nazari a kan kira da sakonnin wayar talho a yankin Magumeri
Sojojin Najeriya masu yaki 'yan kungiyar Boko Haram

Bisa ga alamu, sace ma’aikatan jami’ar Maiduguri (UNIMAID) da sauran mutanen, akwai yiwuwar za a iya samu jinkiri ga wa’adin da babban hafsan sojoji ya bayar cewa dakarun tsaro su gaggauta kama shugaban kungiyar Boko Haram da rai ko matattu saboda a na sa ran an kai mutanen sansanin da shugaban ‘yan ta’addan yake.

KU KARANTA: Rundunar Sojin Najeriya ta bada hakuri game da wani rahoton karya da ta fitar

Wani jami'in leken asiri ya ce: " Dole ne wasu shawarwarin da sojoji suka yanke ta mu goyon baya da kuma amincewar shugabanin na siyasa kafin a aiwatar da su".

Idan dai baku manta ba Legit.ng ta kawo muku rahoto cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun sace mutanen da kamfanin man na kasa NNPC ta hayo don nemo mai a jihar Borno, tare da masu tsaron su da kuma wasu ma’aikatan jami’ar Maiduguri.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel