Nakasa ba mutuwa ba: Kalli abin al’ajabin da wata gurguwa keyi da ƙafafunta (Hoto)

Nakasa ba mutuwa ba: Kalli abin al’ajabin da wata gurguwa keyi da ƙafafunta (Hoto)

Ikon Allah ya wuce tunanin bil Adama, dama idan Allah ya hanaka ta wata hanyar, sai ya bude maka wata hanyar ta daban, shi yasa bahaushe ke cewa wani hanin daga Allah baiwa ne.

Wata budurwa yar kasar Iran mai suna Fatemeh Hamami wanda ta samu nakasa a hannayenta da kafafunta, har bata ko iya tsayawa akan kafa balle tayi tafiya, sai dai Allah ya baiwa wannan budurwa baiwar iya zane.

KU KARANTA: Menene dalilin da yasa aka kashe Ahmadu Bello Sardauna?

Sai dai abin mamakin anan shine, Fatemeh Hamami tana amfani da kafa ne wajen yin duk wani zane da zata yi, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Nakasa ba mutuwa ba: Kalli abin al’ajabin da wata gurguwa keyi da ƙafafunta (Hoto)
Fatemeh

Gidan talabijin na Press Tv ne suka dauko rahoton wannan yar budurwa, bayan ta zana hoton shahararren dan wasan kwallon kafa dake kungiyar Real Madrid, kuma mai rike da kambun gwarzon dan kwallon duniya, Cristiano Ronaldo da fenti mai kyau.

Jama’a da dama sun yaba da kokarin Fatemeh, inda wasu ke sha’awar ganin an nuna na dan wasa Ronaldo wannan hoto, ganin cewa shi mutum ne mai jin kan jama’a wata kila ya baiwa budurwar kyauta gwaggwaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Yadda wani dna takaran Ciyaman yayi mutuwar bagatatan: Kalla,

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng