Yaran mu suna abu wani iri- Iyaye

Yaran mu suna abu wani iri- Iyaye

- Yaran makaranta sun koma asibiti a yau

- Wadaanda suka sace mu sun koya mana addu'a'

Iyayen yara shida makarantar Model College dake jihar Lagas, wanda aka saki a ranar Jumma'a, bayan sunyi kwana 64 tare da masu garkuwa, sun fara bayyana fargaba kan wasu sabbabin halaye da 'ya'yansu ke nuna wa.

Sun kuma ce bayan 'ya'yan sun dawo, sai suka zama masu son ibada sosai.

Mafi yawa daga cikin iyaye sunyi magana a kan sakaye sunansu, iƙirarin cewa jami'an tsaro sun sa masu idanu da kuma cewa anyi masu gargaɗi cewan kar suyi magana da 'yan jarida.

Yaran mu suna abu wani iri- Iyaye
Yaran mu suna abu wani iri- Iyaye

An kuma hana su tilasta 'ya'yan suyi masu bayani akan zaman su da masu satan yaran, da kuma ba da damar 'yan jarida suyi magana da su.

Dalibai shida da aka sace a watan Mayu 25, daga dakunan kwanan dalibai, da mayakan jagorancin Janar America. A cewar iyayensu,suna nuna wasu halayya na son yin sallah.

KU KARANTA KUMA: Rashin Buhari daga Najeriya na tsahon kwanaki 78 ya zama batu na jarrabawa a CNN

Daliban sun yi kwana 64 a wajen marasa cigaban tattalin arziki na garkuwa da mutane kafin a cetosu a ranar Jumma'a daga jihohin Lagos, Delta da kuma Ondo. Gwamnatocin jihohin su uku sun taimaka da kuma goyon bayan jami'an tsaro a cikin manufar.

Tsawon kwanaki da 'ya'yan sukayi tare da masu garkuwa da mutane ya damu iyaye, jami'an tsaro, masana tsaro da kuma 'yan Najeriya gabaki daya. Mutane da yawa sunyi mamaki da abin da zai canza halayen daliban.

Daliban su shida sun hada da, Agbaosi Yahuza, Jonah Bitrus, Philips Pelumi, Adebanjo George, Yusuf Faruq kuma Ramon Isiaka - sun kasance a cikin zaman talala har Jumma'a.

Biyu daga cikin ubanninsu jiya suka bayyana fargaba akan halayen da 'ya'yansu ke nuni. Wadannan mutane sun kasance wani ɓangare na iyaye da cewa sun yi farin ciki a ranar Jumma'a, bayan da suka ji an saki 'ya'yansu da kuma rungume 'ya'yan cikin dadi.

Daya daga cikinsu ya ce: "Akwai wani abu da ba daidai ba tare da ɗana. amma na kasa gane ko menene. Har yanzu muna kiyaye shi. A na kuma kokarin duba Lafiyar sa. Babu hanyar da yara za su je irin wannan wuri ba tare da wani yiwuwar rashin lafiya a jikinsu ba, ko da yake mun gode wa Allah."

Na biyu mahaifin ya bayyana damuwa akan dansa ta wurin hankali, ya ce ya lura da cewa ɗansa baya cikin hankalinsa har yanzu.

A wata magana da tangarahu, wata uwa ta bayyana abin da danta ya gaya mata.

Ta ce: "Ɗana ya gaya mini cewa, sun yi musu barazana kawai sau daya. Ya ce sun yi wasa da masu garkuwa da mutane masu dadi da kuma marasa dadi.Ya ce cewa mazan suna nuna musu kulawa da kuma so agaresu a wasu lokuta.

"Kamar yadda suka koma daga wani maboya zuwa wani,daya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya koya masu yadda zasu yi ruwa,da kuma yadda zasu bi jikin ruwa suje duk inda zasu."

Matan ta kara da cewa yaran su ke dafa abinci da kansu a jagorancin Rotimi, daya daga cikin daliban da aka sace. Su kuma yi wanka da ruwa daga dajin.

Agbaosi ya ce ko da yake Yahuza ya riga ya bayyana min komai da ya faru a wurin boyar,amma ya ce ba zai so ya bayyana shi a yanzu ba saboda an yi musu gargaɗi yin magana da 'yan jarida.

Ya kara da cewa: "Na kasance mutun mai farin ciki a yau. tun da aka sake dalibai da aka sace,ina ta samun hawan jini. Amma lokacin da na karbi labarai cewa an sake su, nan da nan na sami sauki na matsalar jini. Iyalina da da ni mun kasance a cikin duhu a watanni biyu, amma a lokacin da na kafa idanuna a kan ɗana, farin ciki ya mamaye ni.

"Ina da 'ya'ya uku a makarantar - biyu maza da kuma wata yarinya. Biyu daga cikinsu,na miji da mace, suna a SS1, zasu SS2. Isiaka, wanda aka sace, shi ne a SS2 zai shiga SS3. "

Wani iyaye, Mr. Jonah, ya bayyana cewa a lokacin da ya ji daga bakin dalibai cewa an 'saki yaran sai na durkusa a kan gwiwoyi na da kuma gode wa Allah.

Jonah ya ce: "Ina kan gwiwoyi a lokacin da wasu daga cocin mu, da suka ji game da sakin yaran, suka zo suka iske ni akan gwiwa,sai suma suka durkusa suna tayani gode wa Allah. "

Wata uwar daya daga cikin wadanda aka ci zarafinsu, Mrs. Toyin Filibus, ta ce da farin ciki: "Na kasance a gida a lokacin da na ji labarai na ɗana, da sauransu. Abin da ya ba mu mamaki mafi shi ne cewa ɗana ya kira mu zuwa falo a wannan safe don yin addu'a. Lokacin da na tambaye shi dalilin da yasa ya canza, sai ya amsa da cewa ya kasance wanda ko da yaushe ya jagoranci salla a cikin maboyar. Ya ce cewa wadanda suka sace su suna kiranshi 'Fasto.' Ya kuma ce sun kula dasu sosai,kuma suna basu duk abinda suke so. "

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel