Dandalin Kannywood: Duk wanda ya kara cewa na ciwo HIV Allah ya isa - Zainab Indomie

Dandalin Kannywood: Duk wanda ya kara cewa na ciwo HIV Allah ya isa - Zainab Indomie

Shahararriyar jarumar nan ta wasan fina finan Hausa wadda tauraruwar ta ta dan kwanta watau Zainab Indomie ta ce duk wanda ya kara cewa tana fama da ciwon kanjamau Allah ya isa.

Jarumar wadda a kwanan bayanan nan hotunan ta suka rika yawo ta rame ta tsomale bayan ta sha fama da matsananciyar rashin lafiya mai tsawo.

Dandalin Kannywood: Duk wanda ya kara cewa na ciwo HIV Allah ya isa - Zainab Indomie
Dandalin Kannywood: Duk wanda ya kara cewa na ciwo HIV Allah ya isa - Zainab Indomie

Legit.ng dai ta samu labarin cewa alokuttan bayan dai da jarumar Zainab Indomie bata da lafiya mutane da dama musamman yan masana'antar fim din sunyi ta tofa albarkacin bakinsu akan rashin lafiyar tata.

Wasu daga cikin jaruman suna tsogumin cewa kanjamau AIDS ko HIV Zainab ta jajibowa kanta wasu kuma suka ce asiri sababbin jarumai mata suka yi mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng