Dandalin Kannywood: Sana'a 1 da tafi yin fim kawo kudi - Inji Adam Zango
1 - tsawon mintuna
Shahararren jarumin nan na wasan finafinan Hausa kuma mawaki dake a arewacin Najeriya Adam A. Zango ya bayyana cewa a duk Najeriya sana'a daya ce kawai tafi harkar fim kawo kudin kashewa.
Shahararren jarumin ya bayyana cewa harkar man fetur ce kawai ke kawo kudin da suka zarce na harkar fin a kasar nan a cikin wata zantawar da yayi da gidan rediyon nan na BBC.
Legit.ng ta samu labarin cewa jarumin kuma har ila yau ya bayyana cewa fim din nan nasa na Gwaska ya kawo masa makudan kudade fiye da duk yadda ya taba samu a fina finan sa na baya.
Haka ma jarumin ya bayyana wakar nan ta 'Gumbar Dutse' da ta shahara a bakunan mutane a arewacin kasar a matsayin wadda yafi so a cikin dukkan wakokin sa.
Asali: Legit.ng