Jigawa: Hadarin mota ta halaka mutane 18 a Jigawa

Jigawa: Hadarin mota ta halaka mutane 18 a Jigawa

- Akalla mutane 18 ne suka mutu a wani mumunar hatsarin mota a hanyar Gumel zuwa Gugunju a Jigawa

- Mutane 15 ne suka mutu nan take bayan da wani maotar J5 bas ta buga motar tipper daga baya

- Hukumar ta FRSC a jihar tace ta fara binciken don gano dalilin abkuwar wannan hadarin

Akalla fasinjoji 18 ne suka mutu a wani hatsari tsakani motar tipper da wani J5 bas a hanyar Gumel zuwa Gugunju a karamar hukumar Gumel da ke jihar Jigawa.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, babban kwamandan hukumar ta FRSC a jihar, Mista Angus Ibezim, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 29 ga watan Yuli. Ibezim ya ci gaba da cewa wani direba na tipper mai lamba No. XY 744 GRK ya yi watsi da motar yayin da ta baci a kan hanya sakamakon hakan yasa direba na bas ya buga motar tipper daga baya.

Ya ce mutane 15 a cikin motar bas har da direba suka mutu nan take yayin da wasu mutane 3 suka ji rauni.

Jigawa: Hadarin mota ta halaka mutane 18 a Jigawa
Babban kwamandan hukumar ta FRSC a jihar Jigawa, Mista Angus Ibezim

Bisa ga bayanin kwamandan, sauran fasinjoji 3 a cikin motar sun mutu daga baya a asibiti. Ya ce hukumar ta fara binciken don a san dalilin abkuwar wannan hadari. "Muna kokarin gano babban dalilin abkuwar wannan hadarin yanzu”. Inji Ibezim.

KU KARANTA: Menene dalilin da yasa aka kashe Ahmadu Bello Sardauna?

Ibezim ya ce: “Abu na farko da muka zargi shi ne cewa direban na tipper bai sanya wani alamar taka tsantsan da za ta nuna cewa motarsa ta baci. Abu na biyu, muna kuma zargin cewa direban na J5 bas yana mugun gudu ko kuma fitilolin motar ba kyau”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng