Hadin kan kasar nan ya rataya a kan matasa

Hadin kan kasar nan ya rataya a kan matasa

-An bukaci matasa da tabbatar da zaman lafiya a kasar nan

- A shirye muke da mu taimakawa matasa don dogaro da kansu

- Al'adar kasa ta ta kai ni inda ban taba tsammanin bi

Mai magana da nyawun makadashin shugaban kasa, Loulu Akande ya ce "wannan gwamnatin a shirye take da ta tallafawa matasa don samar da zaman lafiya ga matasa".

Hadin kan kasar nan ya rataya a kan matasa
Hadin kan kasar nan ya rataya a kan matasa

Ya bayyana haka ne ranar da jumma'a, lokacin da ya karbi bakwancin wata mawakiya 'yar najeriya mazauniyar kasar waje, Abiodun Koya a ofishinsa". Koya ta kai wa mukadashin shugaban kasa ziyarar ba zata ne, ta mika masa sabuwar wakar da ta yi wa kasar mai taken " Mu tallafawa kasar" 'Lift up Nigeria', a cikin wakar akwai na murnar bakin cika shekaru 57 da bakwai da samun 'yancin kasar.

Mukaddashin shugaban kasa ya ce "yana da matukar muhimmanci mu tallafawa Matawan kasar nan, saboda kyakkyawar mu'amalar da take tsakanin mu da matasa, a matsayin su na kashin bayan al'umma.

KU KARANTA: Wani hatsarin mota ya yi sanadiyar halaka rayuka 18 a jihar jigawa

Wannan dalili ne ya sa fadar shugaban kasa, za ta shirya nauyin kaddamar da wakar da Akande ta yi.

Ya kara da cewa: "Wannan gwamnati za ta yi , iya kokarin ta wajen tallafawa matasa, ko da wani irin basira da mutum yake da ita. Sannan muna kira ga daukkan matashin da yake da wata baiwa da za ta taimaki al'umma, mawaki ne, ko marubuci ne, ko jarumi ne, da sauran bangarorin rayuwa, da su yi anfani da su wajen had in kan al'ummar kasar nan. Abu ne mai kyau da gwamnati za ta yi alfahari da shi, na taimakon matasa domin su ma su taimaki al'umma, ba tare da la'akari da kabila, ko harsher, ko kuma addini ba matukar sako zai isa yadda ya kamata ga sauran al'umma."

Koya 'yar Najeriya ce, ta yi shekaru 18, a kasar turai, ta ce "Fata na shi ne wannan waka ta zama sanadiyar canza zukatan al'umma da nasarar kasar kasar nan." Ta kara da cewa wannan wakar da ta yi ubangiji ne ba ta iya, saboda haka wakar ya kamata a dauke ta da muhimmanci.

Koya ta yi kira ga al'umma da su hada kansu wuri guda, ubangiji da ya yi mu, shi ya san dalilin hada mu wuri guda, saboda haka mu hada kanmu wuri guda domin ci gaban kasar nan. Najeriya ta zama ruwa ma ba da mama wa al'ummar Afirka ta bangaren siyasa, kasuwanci, rike al'adu, kwalliya, da sauran abubuwan more rayuwa, wannan ya sa kowa yake Shi'awar yin koyi da kasar.

Na samu nasarori da dama, na he kasashen duniya da dama, ta sanadiyar waka. Na yi nasarar samu wadannan ne, ta saniladiyar riko da na yi wa al'adar kasa ta hakane ya sa kowa yake sha'awar abin da na yi, kuma ake kwaikwayon abin da na yi.

Abiodun Koya fitacciyar mawakiya ce a kasar Turai, ta yi manta mutane waka da suka hada da; shuagabannin kasashe, 'yan majalisun kasar Turai, da sarakunan, da Jakadodin kasashe da Dama, kuma iya ce 'yar najeriya da ta yi nasarar wake shuagabannin kasar Turai su 2.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

KO KU SAME MU A https://www.facebook.com/naijcomhausa

KO A http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel