Sanin Kimiyya: Sauro da Kuda, Wanne yafi cutar da jama'a?

Sanin Kimiyya: Sauro da Kuda, Wanne yafi cutar da jama'a?

A rayuwarmu dai ta duniya, akwai abokan zama da muka tsana, amma kuma kut-da-kut suna makale da mu, in basu, watakil bamu, amma kuma muma watakil in bamu, basu. Da kuda namu na gida, da sauro, shin wanne ne yaffi illa? Wanne ne kuma da da hali zaku so rabuwa da shi?

Zazzabin cizon sauro, yafi kowacce irin cuta da annoba hallaka bil-adama a duk tarihin rayuwar duniya, haka kuma yafi kashe kananan yara, har ma da na ciki. A yanzu kimiyya ta gano ashe lange-lange ne yake jawo ta. Milyoyi ke mutuwa a duk shekara a kasashe masu dumi, na kusa da tsakiyar duniya wato equatorial/tropical climates a turance.

Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?
Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?

Zazzabi dai a zamanin da ba'a ma san me yake kawo shi ba, an dai zata asirin makiya ne, ko kuma zunubbai ne suka yi wa mutum yawa, kamar dai yadda ake wa sauran cutuka wannan zargi. Akwai ma karin maganar cewa, in kaga ka dade baka yi rashin lafiya ba, wai ka binciki imaninka.

Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?
Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?

A duk shekara a misali, Najeriya tana kashe biliyoyin daloli don kawai sayo maganin zazzabi, wanda da yawa ma ya dena jin maganin, dalilin rashin shanye maganin yadda likita ya fadi, musamman in an sami sauki. Ita dai kwayar tcutar, takan kwanta a hanta, ta gyagije ta dawo da karfi iye da na da. Har wa yau kuma, babu alamar sauro zai rabu da Afirka, da sauran kasashe masu dumin yanayi, saboda rashin tsari, kazanta, da kasa fahimtar yadda za'a yake shi.

KARANTA KUMA: Shin da kwakwalwa da zuciya, wacce ake amfani da ita wajen tunani

A bayan zazzabin malariya, an gano cewa wata cuta da a da ake dauka kamun aljannu ce, saboda kadawar idanu suyi ruwan dorawa, fata tayi baki kirin, ita ma ashe sauro ke jawo ta. Wannan cuta ita ce Yalo fiba. wato Yellow fever, wadda tuni an kawar da ita a doron kasa.

Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?
Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?

Sauro kuma a sabon bincike ma a kasar Amurka, ashe shi yake jawo haihuwar 'gwai-gwai', irin yaran nan masu karamin kai da a da ake cema 'yan ruwa ko 'ya'yan aljannu. Yana yada wata cuta ne a jinin mace mai ciki, wadda takan hana kwakwalwar dan tayin habaka tun a ciki. Ana kiran kwayar cutar Zika Virus.

Sauro dai mugun kwaro ne, to amma kuma yana cikin halittu da ke da muhimmanci ga tsanin abinci da ake kira food chain daga ecological balance, wato daidaiton halittu da duniyarsu.

A misalin wannan tsani, zamu iya dauka bamu bukatar wata halitta don bamu ga amfaninta ba, amma kuma mun dogara da ita a rayuwa. Kamar a ce kudan zuma, wanda shi yake yada da yawa daga 'ya'yan furanni na tsirrai da ke bamu abinci lokacin girba.

LEKA WANNAN: Albashi mafi karanci na talakka, duba yadda kasashe suka sha kan Najeriya

A irin wannan tsani, an gano cewa sauro abinci ne na da yawa daga dabbobi na daji, kamar jemage, da kifi a ruwa, musamman ma kwayayen sauron, wadanda a ruwa yake yinsu. Mu kuma gashi muna son kifi sosai.

Sauro, idan ya balaga makonni uku kawai yake yi kafin ya mutu. Amma a wadannan makonni, barbara daya tal ta ishi macen haihuwar kwayaye daruruwa a ruwa kwantacce. Tana da dai jakar adana maniyyin namijin ne, inda duk lokacin da kwayayenta suka shirya, sai ta diga musu maniyyin da kanta. Haka kuma, macen sauro, itace mai son jini, namijin ba ruwansa da kai.

DUBA WANNAN: Labarin matar shugaba Buhari ta farko

Kuda dai, yana yada cutuka iri-iri, musamman amai da gudawa, mai kisa nan take. Amai da gudawa dai na yaduwa ne da taimakon kudaje har ta zamo annoba. A kowanne lokaci kuda kan hau mana kwanuka da abinci, da jiki, bayan ya gama yawo kan bayan gida da kazanta, ya kwaso kazanta da cutuka, sai kawai yazo kuma ya watsa su a ko'ina.

Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?
Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?

Tsabar iya shege na kuda, idan ya sami kazanta kamar kashi, bayan ya ajje kwayayensa domin 'ya'yansa su kyankyasa, wadanda su ke zama tsutsa kafin su zamo kuda balagagge, sai kawai ya kwashi kananan halittu masu rai, masu kuma kawo cuta ga mai-rai, wato bacteriya, yayi ta watsawa a jikinsa, kamar yana alwala, ya zuba su a koina. fiffike, kafafu, wuya, tumbi, da hannaye, ya debo su domin zubawa a wani abincin.

Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?
Sauro da Kuda: Wanne yafi cutar da jama'a?

Dabarar kuda dai wajen yin hakan shine, idan ka bar abinci a bude, yazo ya ci, ya kuma ajje wadannan cutuka, saboda suyi maza su rubar da abincin domin ya dawo ya ajje kwai, domin 'ya'yansa tsutsotsi su samu lokacin yaye.

Kuda dai ko baya yada cuta akwai damu, da naci, akwai kuma mayata, ga saurin tsiya, baya kwashe da wani alheri a fuka-fukansa sai cutuka, don haka rufe abinci yafi fa'ida akan dulmiyar da kudan in ya hau.

ZAKU SO WANNAN: Labarin Hitler da yakin duniya na biyu

Amfanin kuda dai shima bai wuce cewa yana saurin cinye mushe da rubar da shi ba, cinye kazanta da shi da jariransa tsutsotsi. A wasu lokutan kuma, shima yana yada iri domin shuke-shuke.

Kuda dai a tsanin abinci, na food chain, yana ciyar da kadangaru, kwadi, tsaka, kifi, jemagu, da ma tsuntsaye, wadanda mu kuma muka dogara da wasunsu domin abinci, wasunsu kuma ababen nishadinmu su ci, kamar su mage, masu son cin kadangare da kifi.

Kuda dai yana wata uku kafin ya mutu, watau a shekara, rayuwar dangi hudu muke gani. Haka kuma baya son sanyi da tsafta, shi yasa baya damun kasashen turawa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel