Naira 150 ta haddasa kisan wani dan Acaba

Naira 150 ta haddasa kisan wani dan Acaba

Azal ta fada ma wani dan acaba mai suna Rabiu Gaffar wanda har tayi sanadiyar mutuwarsa bayan wani dan rikici da ya shiga tsakaninsa da wani matashi mai shekaru 23 a duniya, Ibrahim Sulaiman akan kudin aikin sa naira dari da hamsin (N150).

Mumunan alámarin ya afku ne a yankin Ajuwon dake jihar Ogun.

Sulaiman wanda ya kasance dan asalin jihar Kogi ya fusata a lokacin da rikici ya kaure a tsakaninsu, inda ya dauki wani katako ya buga wa Gaffar a kai, a nan take ya fadi ba tare da ko ya shura ba.

Tuni ‘yan sanda suka cafke Sulaiman kuma ya amsa laifinsa, sai dai ya alakanta faruwar al’amarin da sharrin shaidan, ya kuma ce ya yi danasani.

Naira 150 ta haddasa kisan wani dan Acaba
Naira 150 ta haddasa kisan wani dan Acaba Hoto: Rariya

A cewar shi “Har yanzu ina cike da alhini. Ban san me ya faru da ni ba. Shaidan ne ya ingiza ni”

Mamacin ya bar mata da yaro guda daya.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya matsu ya dawo gida – Gwamna Ortom ya yi Magana bayan ziyarar Landan

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce za su gurfanar da mai laifin da zaran sun kammala bincike.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

Don bamu shawara ku aiko mana da labarai, tuntubemu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng