An saki hotunan sojojin da suka mutu wurin ceton ma’aikatan NNPC da akayi awon gaba dasu
- Sojoji 12 suka rasa rayukan su
- Dangin wa'yanda aka kashe suna zaman makoki
- An ceto duka ma'aikatan NNPC da aka yi awon gaba dasu
An fitar da Hotouna sojojin da yan Boko-haram suka kashe lokacin da suka je ceto masu hako mai a Borno. Legit.ng ta rawaito cewa an kama mutanen ne kusa da wani kauye Jibi a karamar hukumar Gubio a ranar Alhamis 20 ga wata Yuli, har da yan kungiyan Civilian-JTF aka kashe
Washegarin ranar da akayi awon gaba da mutanen, mai Magana da yawun sojojin Najeriya Brig.Gen Sani Usman ya fitar da wani jawabi a ranar Laraba 27 ga watan Yuli cewa duka ma,aikatan NNPC da aka sace a ranar talata an ceto su.
Legit.ng ta rawaito cewa akalla sojoji 12 aka kasha sai kuma ma’akatan Jami’an Maiduguri 4 suka ra ran su.
Dangin sojojin da aka kasha suna zaman makoki. Sunayen sojoji da suka rasa rayukansu a harin sune
KU KARANTA: Keyamo ya kai hari ga wadanda sukayi ikirarin cewa shugaba Buhari na cikin wani yanayi
Dr Milicus Joseph daga Geology Dept, Idris Abubakar Njodi da kuma Dr Daniel Birma na Dept of soil Science. Sojijin sun sadakad da rayuwan su ne dan ceto ma’aikatan NNPC
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ko ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng