Dandalin Kannywood: Yin fim tsaftatacciyar sana'a kamar ta kowa - A'isha Tsamiya
Fitacciyar jarumar nan na wasan fina-finan Hausa watau Aisha Aliyu wadda aka fi sani da Aisha Tsamiya ta bayyana cewa ita fa ta dauki fim a matsayin sana'a shi yasa ma ta tsunduma ciki ka'in-da-na'in.
Jarumar dai ta bayyana hakan ne ga majiyar mu ta sashen Hausa na BBC inda ya ce ita dama can tun tana karama harkar fim din tana burge ta kuma masu yin fim din suna burge ta.
Legit.ng dai ta samu labarin cewa Aisha Tsamiya ta fara yin fim ne sosai tun a shekara ta 2011, sannan kuma ta kara da cewa dukkan jaruman da ke yin fim tare da ita suna burge ta.
A kwanan baya dai mun kawo labarin yadda a sallar da ta wuce jarumar ta sha ruwan duwatsu daga wasu mafusatan matasa a lokacin da ta makara zuwa wani wasan salla.
Asali: Legit.ng