Za mu sai wa Sarkin musulmai gidan naira miliyan 700 a Abuja - Gwamnatin jihar Sokoto

Za mu sai wa Sarkin musulmai gidan naira miliyan 700 a Abuja - Gwamnatin jihar Sokoto

Mahukunta a cikin gwamnatin jihar Sokoto dake a arewa maso yamman Najeriya sun bayyana cewa makudan kudaden nan da suka kai naira miliyan 700 da ake ta cece-kuce kan su gida za su siya wa sarkin musulmi da su.

Wannan bayanin dai na zuwa ne bayan da hukumar nan dake hana cin hanci da rashawa ta tarayya watau EFCC ta bankwado wata harkallar makudan kudade dake shirin faruwa a tsakanin asusun gwamnatin jihar Sokoto da kuma Kabiru Tafida.

Za mu sai wa Sarkin musulmai gidan naira miliyan 700 a Abuja - Gwamnatin jihar Sokoto
Za mu sai wa Sarkin musulmai gidan naira miliyan 700 a Abuja - Gwamnatin jihar Sokoto

Legit.ng dai ta samu cewar an saki Kabiru Tafida bayan matsi da hukumar EFCC ta samu daga gwamnatin jihar Sokoto da fadar Sarkin Musulmi tun ranar Talatar da ta wuce da ya gurfana a gaban hukumardomin bata bayanai kan harkallar shiga da ficen wadannan kudade.

Talakan Najeriya dai na kallon wadan nan kudi a matsayin wadan da suka yi yawa musamman ma ganin halin da yake ciki na matsi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel