Muna rokon gwamnati da ta halasta sana'ar mu - Karuwan Najeriya

Muna rokon gwamnati da ta halasta sana'ar mu - Karuwan Najeriya

Wata shahararriyar mai sana'ar karuwanci kuma shugabar kungiyar karuwan Najeriya mai suna Amaka Anemo ta mika kokon barar kungiyar ta ga gwamnatin tarayya inda ta bukaci da a halasta sana'ar su.

Shugabar dai a bayyana cewa halasta sana'ar tasu abu ne mai matukar anfani da muhimmanci musamman ma yanzu dake ta hankoron ganin an rage yaduwar cutar nan mai karya garkuwar jiki watau HIV.

Muna rokon gwamnati da ta halasta sana'ar mu - Karuwan Najeriya
Muna rokon gwamnati da ta halasta sana'ar mu - Karuwan Najeriya

Legit.ng ta samu daga shugabar cewa ita abun da ke bata mamaki ga mutane shine yawancin masu sukar sana'ar ta su duk muna fukai ne don kuwa sun dawowa suyi anfanin da su idan sun bukata.

Mutanen gari dai na ganin wannan bukatar tasu da wuya ta samu shiga a Najeriya don kuwa dukkan manyan addinan kasar sun haramta yin karuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng