An nada jihar Lagas ta 4 a masu kudin Afrika: Tana da biloniya guda 4

An nada jihar Lagas ta 4 a masu kudin Afrika: Tana da biloniya guda 4

Jihar Lagas, tsohuwar tarayyar Najeriya ta zo ta hudu a biranen da suka fi arziki a nahiyar Afrika.

Ba tare da an ambaci wani birni a cikin birane goman da sukayi nasara ba, matattarar kasuwanci ta kasar ta kasance wacce tafi ko wane arziki a tsakanin manyan biranen Najeriya.

A wani rahoto daga bankin AfrAsia da kuma New World Wealth, Lagas zata je gida da dalan Amurka biliyan 120 (US$120 billion), guraren da suka dara ta sun hada biranen kasar Afrika ta Kudu guda biyu, Johannesburg, Cape Town da kuma birnin kasar Masar wato Cairo.

Wannan jiha ta Najeriya tafi ko wanne shahara a kasar.

An ambaci biloniyan daloli guda hudu dake zaune a jihar Lagas, tare da masu ninkin miliyoyi 360 da kuma masu miliyoyi 6,800.

An nada jihar Lagas ta 4 a masu kudin Afrika: Tana da biloniya guda 4
An nada jihar Lagas ta 4 a masu kudin Afrika: Tana da biloniya guda 4

Two Forbes-recognized wealthiest Nigerians, Femi Otedola of Zenon Oil and Mike Adenuga of Globacom reside in Lagos.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo zai rantsar da sababbin ministoci gobe

Mutane biyu da aka ambata a matsayin ýan Najeriya wadanda siuka fi arziki sune Femi Otedola na Zenon Oil da kuma Mike Adenuga na Globacom dake zaune a Lagas.

Mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote ma na da hannun jari a birnin.

Rahoton yace anan ana Magana ne kawai a kan dukiyoyin mallakin masu kasuwanci dake zaune a ko wani birni. Ya hada da dukiyoyinsu, kudadensu da kuma kasuwancin su. An ware kudaden gwamnati daga ciki.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

Don bamu shawara ku aiko mana da labarai, tuntubemu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel