Daga ƙarshe, an gano maganin cutar Ƙanjamau a Afirka, Karanta

Daga ƙarshe, an gano maganin cutar Ƙanjamau a Afirka, Karanta

- Wani karamin yaro ya samu waraka da cuta mai karya garkuwa jiki

- Daga shan kwayoyin rage radedin ne yaron ya warke

Wani karamin yaro wanda aka haife shi dauke da cutar kanjamau a kasar Afirka ta kudu ya tsallake rijiya da baya, inda ya warke daga muguwar cutar mai karya garkuwar jiki.

Sai dai dama a kasar ta Afirka ta kudu, yawancin masu fama da wannan cuta sukan dogara ne ga shan kwayoyin maganin rage radadin cutar, amma cikin ikon Allah sai gashi yaron mai shekaru 10 ya samu waraka ta hanyar shan wadannan kwayoyi.

KU KARANTA: Abinda Buhari ya faɗa min a lokacin da na keɓe da shi a birnin Landan – Inji Nasir El-Rufai

An tabbatar da samun warakar yaron ne bayan kula da bacewar dukkanin alamomin da masu dauke da cutar ke fama dasu, kamar yadda shugaban taron kungiyar masana cutar kanjamau Linda- Gail ta bayyana yayin taron nasu.

Daga ƙarshe, an gano maganin cutar Ƙanjamau a Afirka, Karanta
Kwayar cutar Ƙanjamau

Shi wannan yaro da aka haifa a shekarar 2007 ya kamu da cutar ne daga wajen mahaifiyarsa a jim kadan bayan ta haife shi, hakan tasa iyayensa nuna farin ciki sosai, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Wai kodai Buhari ya mika mulki ga Osinbajo ne? Kalla:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng