Mafi karancin albashi a sauran kasashen duniya, dubi inda aka yiwa Najeriya nisa

Mafi karancin albashi a sauran kasashen duniya, dubi inda aka yiwa Najeriya nisa

- A yanzu dai mafi karancin albashin N18,000 a Najeriya ya zamo kudin yini daya, a wasu jihohi ma N7,000 ne albashi mafi karanta, duk da kungiyar kwadago ta saka kaimi wajen ganin an kara wa ma'aikata albashi zuwa N54,000, hakan baya nufin zamu kai wasu kasashen.

Kafin zuwan wannan gwamnati ta APC dai dala na chanji ne daga N160 zuwa N199 a kasuwar chanji. Amma faduwar farashin mai ta shafi wannan chanji, da ma kuma rashin sanin alkiblar sabuwar gwamnatin na dogon lokaci bayan hawansu, ya jefa tattalin arzikin kasar cikin tambal-tambal.

Mafi karancin albashi a sauran kasashen duniya, dubi inda aka yiwa Najeriya nisa
Mafi karancin albashi a sauran kasashen duniya, dubi inda aka yiwa Najeriya nisa

A waiwayen Legit.ng na yau, mun dubo muku yadda wasu kasashen suke karbar albashi, da kuma ma nawa suke karba a wata a kwatankwacin Naira.

Fahimtar cewa a kasashe da suka ci gaba, akwai tsadar rayuwa, da kuma tabbacin arashi, inda abu da ka siya bara ukku, zaka iya samunsa a farashinsa bai chanja ba, ba kamar mu ba, kullum hauhawar farashi na kara yaduwa, wannan zai sa a fahimci dalilin saukin rayuwa ko rashinsa a Najeriya.

1. Najeriya dai na biyan N18,000 ne a matsayin albashi mafi karanta, wanda idan aka juya zuwa dala a yadda chanji ya kama a kan N360, kusan kamar muna karbar $50 kacal a wata daya.

2. A Amurka, inda ake biyan dala $11 a aikin awa daya a rana, in ka lissafa zaka sami $88 kenan a aikin yini, wanda in ka juya zuwa ranakun aiki 20 a wata zaka sami $1,760 kenan, a matsayin albashi mafi karanta, wanda yayi daidai da N633,600 a wata a naira kenan. Wannan yana nufin lebura mafi kankantar samun kudi zai sami fin rabin miliyan a aikin wata.

DUBA WANNAN: Sanata Kwankwaso ya tafi kasar masar ceto, wa yaje cetowa?

3. Kasar Belgium na bada $1,738 wanda ya kama N625,000 na naira, fin rabin miliyan kenan a mafi kankantar albashi.

4. New Zealand na bada $3, 187 a wata a matsayin albashi mafi kankanta. Kwatankwacin N1,147,320 kenan, wato mafi karancin albashi ya fi naira miliyan daya kenan.

5. Japan, $1,000 watau naira N360,000 kenan.

6. Switzerland, wadda ta fi kowa, dala $5,600. Watau fa naira miloyan biyu kenan ga talakkan kasa, albashi mafi kankanta kenan. A shekara kuma kenan kusan miliyan 24 kenan, banda bonus.

A baya ma dai anyi ta tafka muhawara a majalisun kasar kan dagewar gwamnati cewa lallai sai ta baiwa marasa aikin yi mafi kankantar albashi saboda zaman banza, amma su kansu talakawan suka ce basu amince ba, aka yi ta zanga-zanga a bara, a 2016 da kuma a baya a 2011.

ZAKU SO WANNAN: Tarihin uwargidan shugaba Buhari ta farko

Su dai jama'ar kasar sun amince cewa biyan kudin zaman banza zai kara musu lalaci, basu kuma so gwamnati ta kara kudin domin za'a tatsa ne daga masu kudi. Akwai kuma tsoron bakin haure daga kasashen talakawa, muddin suka ji wannan garabasa.

Kasar Switzerland ce mai bankin duniya, kuma nan ne manyan barayi daga gwamnatocin duniya kan kai kudaden kasashensu su boye. Kasar Swiss ita ce kasa mafi zaman lafiya a duniya baki daya.

DUBA WANNAN: Abubuwa 10 da ya kamata ku sani kan yakin duniya na 2

7. Denmark $1,820, N655,200 a wata.

8. Luxembourg $2,500, wato N900,000.

9. Spain $760, watau 276,000.

10. Kasar Chadi mai makwabtaka da jihar Borno ma dai, $120, watau N43,000. Watau ko kasar Chadi ta ninka mu a albashi sau ukku.

Wadannan alkalumma na nuna iyaka ma wadanda ke iya samun albashin kenan, sanin kowa ne a kasar Najeriya mai yawan talakawa basu ma da aikin yi, da wadanda suka je makarantar balle ma wadanda basu je ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel