Labarai cikin hotuna: Gwamnatin jihar Kebbi za ta baiwa duk wani dan ta'adda da ya tuba sana'a
- Gwamnatin jihar Kebbi za ta tallafawa duk wani dan ta'adda da ya tuba
-Wannan yunkurin kan iya janyo duk wani mai ta'addaci a jihar ya tuba
Jaridar Legit.ng ta samu rahoton nan ne shafi sada zumunta na twitter.
KU KARANTA: Gurbatattun 'yan siyasa su na amfani da Boko Haram
Gwamnatin jihar kebbi za ta tallafawa duk wani dan ta'adda da ya tuba da yin ta'addaci a jihar ta da sana'a wadda za su samu abin yi, ta yi wannan yunkurin ne don kawo karshen ta'addaci a jihar ta, kuma wannan zai taimaka wajen rage faruwar miyagun laifuka a jihar don daman rashin aiki ne yake jefa da yawa daga cikinsu cikin hakokin Allah wadai.
Ireren makamai da aka karba wanda yan ta'adda suka sallamawa gwamnatin jihar, don su ma sun ji dadin wannan yunkurin da gwamnatin ta kawo musu.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng