Labarin wata budurwa da ta kubucewa 'yan kungiyar asiri

Labarin wata budurwa da ta kubucewa 'yan kungiyar asiri

- Yadda wata budurwa ta ba da labarin kubucewa 'yan kungiyar asiri a jihar Legas

- Wannan budurwa dai ta yi sa'a akwai kwananta a gaba

Wata budurwar lauya, Jemaimah Kalu ta zayyano labarin yadda ta kubuce daga hannun 'yan kungiyar asiri da suka dauke ta.

Labarin wata budurwa da ta kubucewa 'yan kungiyar asiri
Labarin wata budurwa da ta kubucewa 'yan kungiyar asiri

Jemaimah ta bayyana cewa tun a lokacin da take karatun ta na zama lauya, a kan hanyar ta komawa makarantar koyon alkalanci ta jihar Legas ne ta fada hannun 'yan kungiyar asiri.

Ta bayyana cewa, ta shiga motar tasi wadda a cikinta akwai fasinjoji guda uku maza har da direban daga gadar Falamo zuwa cikin birnin Legas.

Shigarta wannan mota ke da wuya sai suka canja yare suka koma yaren hausa, tsammaninsu ba ta jin yaren, ita sai ta bi yarima a sha kida ta nuna musu babu abinda take fahimta.

KU KARANTA: Wata kungiyar dalibai ta kai karar gwamnatin jihar Kaduna

Direban motar ya yi ta tamabayar su har yanzu ba ta fita hayyacinta bane, ita ko idannunta kuru ko kiftawa.

Da su ka gaji dai sai direban ya tsayar da motar a bakin wata hanya, inda wani daga cikinsu ya fesa mata wani abu a fuska, su ka ga shiru har yanzu ba ta sheme, don a cewar ta tana addu'oi ne a cikin zuciyarta.

A wannan lokaci ne su ka fusata, suka ce wannan ba 'yar hannu bace don ba za ta biya musu bukatar su ba, shine su ka bude kofar mota ta kama gabanta.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel