Majalisar Dattawa ta ba da sunayen magungunan zazzabin cizon sauro guda 42 da aka hana amfani da su
Majalisar Dattawa ta Najeriya ta ba da sunayen magungunan zazzabin cizon sauro wanda aka hana amfani da su a kasar nan.
A yau talata 25 ga watan Yuli, majalisar dattawa ta ba da sanarwar magungunan zazzabin cizon sauro guda 42 da aka hana amfani da su a kasashen turai amma har yanzu hakan bai sa an daina amfani da su a nan Najeriya ba.
Majalisar ta janyo hankalin jama'ar kasar nan akan cewa har yanzu akwai magunguna guda 42 da ake siyarwa a asibitoci da shagunan siyar da magani da dama kuma suke cin kasuwarsu a kasar nan.
A halin da ake ciki, majalisar ta umarci kwamitin kula da harkokin lafiya wanda Sanata Olarewaju Tejuosu yake shugabanta, da su gaggauta bincike a kan wannan al'amari kuma su kawowa majalisa sakamakon binciken na su cikin kankanin lokaci.
Sanata mai wakiltar tsakiyar jihar Abia, Sanata T.A Orji ne ya kawo wannan tattaunawar a majalisar, inda ya bayyana cewa akwai magungunan zazzabin cizon sauro guda 42 da kungiyar yankunan turai wato European Union ta hana kasuwancinsu da amfani da su a gaba daya a gaba daya kasashen yankin turai.
KU KARANTA: Wata kungiyar Dalibai ta kai karar gwamnatin jihar Kaduna
Majalisar ta bada sunayen magungunan kamar haka: Alaxin 60mg tablet (dihydroartémisinine)B/8; Alaxin na ruwa (dihydroartémisinine) FL/80ml; Amodiaquine 200mg compressed B/1000; Amodiaquine 200mg compressed B/1000; kwayoyin Arinate 100mg (artésunate) B/6; Arinate 50mg (artésunate) B/6; Arsumax 50mg (artésunate) B/12; Artemax 60mg, (dihydroartémisinine) B/8; Artémédine 40mg (artemether) B/12; Artémédine 50mg (artemether) B/12; da Artenam 50mg (artemether) B/14.
Suka cigaba da kawosu kamar haka: Kwayoyin Artenam 60mg (artemether) B/8; Artésiane 300mg na kanana yara (artemether) FL/38g; Artésunate 100mg compressed B/120; Artésunate 50mg tablet B/120; Artexin 60mg (dihydroartémisinine) B/8; Camoquin 200mg (amodiaquine) B/9; Camoquin 200mg (amodiaquine) B/25 wanda ake shafawa a jiki.”
Da kuma: Kwayoyin Camoquin 200mg (amodiaquine) B/55; Camoquin 200mg (amodiquine) B/24; Camoquin 600 mg (amodiaquine) B/3; Camoquin na ruwa 50mg/ 5ml (amodiaquine) FL/60ml; Cotecxin na ruwa (dihydroartémisinine) FL/80ml; Cotecxin 60mg (dihydroartémisinine) B/8; Daraprim tablet (pyriméthamine) B/30; da kuma kwayoyin Falcinil 50mg (artésunate) B/12.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na facebook ko twitter a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa/
Asali: Legit.ng