Wata budurwa ta cewa mahaifiyarta ai auren ba dole ba ne

Wata budurwa ta cewa mahaifiyarta ai auren ba dole ba ne

A tsari irin na al'adun nan gida Najeriya duk yariyar da ta isa aure gaba daya dangi za su fara zuba idan su ji wai yaushe wance za ta fito da miji

Kamar yadda aka saba a kasar nan, duka wata yarinya budurwa wadda ta isa aure kuma 'yar gidan mutunci, abin alfahari ne a danginta a ce ai wacca ta fitar da miji.

Wannan ala'adar abun soyuwa ne ga kowane gida koda kuwa addinin kiristanci su ke ballantana kuma gidan musulmai.

An samu rahoto cewa, wata budurwa yar nan kasar Najeriya, Tolu Akanji, ta bayyanawa mahaifiyar ta cewa, ita fa aure ba dole bane, wanda sanadiyar haka ne mahaifiyar ta shiga cikin wani hali na kunci don ganin cewa 'yar da ta haifa ta zata fadi irin wannan.

A tsari duk budurwar da ta isa aure kuma iyayenta su ka tambayeta ko yaushe zata fitar da miji, amsar da ya kamata ta mayar shine kwanannan ko kuma tayi shiru saboda kunya irin ta 'ya mace.

KU KARANTA: Kunji labarin wani dan shekara 50 da ya daina girma tun yana shekaru 5

Sai gashi mahaifiyar Tolu da take ganin ya kamata 'yar ta ta fitar da miji don ta haura shekaru ashirin a duniya, sai ta tambayeta yaushe take sa ran yin aure, amma budar bakinta ke da wuya tace ita fa auren nan ba dole bane, wanda wannan ya sa mahiafiyar Tolu ta dauke ta kai ta cocinsu ko da a bata shawarwari da kuma addu'oi irin na addininsu.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel