Yansanda sun ga bayan ýan fashin da suka addabi garin Bichi na jihar Kano (Hotuna)

Yansanda sun ga bayan ýan fashin da suka addabi garin Bichi na jihar Kano (Hotuna)

Jami’an rundunar yansandan jihar Kano sun hallaka wasu yan fashi har lahira bayan wani musayawar wuta da suka yi daya kwashe mintuna 15 ana fafatawa a kan babbar hanyar Kano zuwa Katsina.

Kaakakin rundunar, Magaji Musa Majia ne ya bayyana haka, inda yace yan fashin sun yi kaurin suna wajen tare hanyar musamman a duk ranar da kasuwar garin Charanchi ke ci, a nan suke kwace ma yan kasuwa kudadensu.

KU KARANTA: Wani Ministan Buhari ya ɗauki nauyin wasu yara ƙanana dake aikin cike ramukan titi (Hotuna)

Hukumar Yansandan ta samu koke koke da dama daga jama’n dake bin hanyar, hakan ta sanya kwamishinan yansanda aikawa da jami’ai na musamman, wanda sune suka yi maganin yan fashin.

Yansanda sun ga bayan ýan fashin da suka addabi garin Bichi na jihar Kano (Hotuna)
Gawawwakin ýan fashin

“Mun gano bindigu kirar AK 47 guda 2, alburusai, adda daga hannun su, sa’annan jami’an mu basu samu wata matsala ba yayin musayar wutan.” Inji Majia

Yansanda sun ga bayan ýan fashin da suka addabi garin Bichi na jihar Kano (Hotuna)
Makaman da aka kwato

Legit.ng ta ruwaito Majia yana kira ga jama’a da su cigaba da taimaka yan rundunar yansanda da bayanai masu inganci da zasu taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu na tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Da gaske Dansanda abokin kowa ne?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng