Wasu mata 3 sun baiwa boka jikkunansu da miliyan 3 don ya musu kudin tsafi, amma ya gagara

Wasu mata 3 sun baiwa boka jikkunansu da miliyan 3 don ya musu kudin tsafi, amma ya gagara

Gaskiyar Malam Bahaushe daya ce garin neman kiba ne ake samun rama, haka ta kasance da wasu abokai su uku wadanda suka hada ma wai Boka kudi har naira miliyan 3 da 600,000 wai don ya hada musu kudin tsafi.

Wannan bayani ya bayyana ne yayin da aka gurfanar da Boka Ibrahim Ifawale gaban kotun majistri dake Ikeja, jihar Legas, inda dansanda mai kara ya tasa keyar Ifawale kan zargin da ake yi masa.

KU KARANTA: Wani Ministan Buhari ya ɗauki nauyin wasu yara ƙanana dake aikin cike ramukan titi (Hotuna)

Dansanda mai kara ya shaida ma kotu cewar Ifawale ya damfari wasu yan mata su 3 Aminatu Bello, Iyabo Popoola da Keji Lawal da sunan zai yi musu tsafi don su samu arziki.

Wasu mata 3 sun baiwa boka jikkunansu da miliyan 3 don ya musu kudin tsafi, amma ya gagara
Wata Kotu

Bugu da kari wannan boka madamfari sai daya kwanta da dukkanin matan su uku, duk cikin shirin yi musu tsafin samun arziki, bayan nan ne fa sai boka Ifawale yayi gum da bakinsa, yacii ya goge baki. Daga nan ne fa yan matan suka kai karar bokan bayan sun fahimci take takensa.

Majiyar Legit.ng, kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito bokan na iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari kan laifin daya aikata.

Sai dai abinka da dan gari, boka Ifawale yayi mursisi ya musanta tuhumar da yan matan ke yi masa, daga nan sai alkalin kotun ta bada belinsa akan kudi N500,000, tare da dage sauraron karar zuwa 20 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Naira miliyan 30 zai maka arziki?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng