Wasu ƙananan yara sun yi mutuwar ban tausayi a garin Kaduna, jama’a sun girgiza (HOTO)
Mutuwa rigar kowa, wani abin al’ajabi ya faru a layin Surajo dake unguwar Tudun Wada Kaduna, inda aka tsinci gawawwakin wasu kananan yara su uku a cikin wata mota bayan kwanaki 2 da bacewarsu.
Kananan yaran su hudu ne suka bar gida tun a ranar Laraba 19 ga watan Yuli, inda aka dinga nemansu ba’a san inda suka shiga ba, sai a ranar Asabar 22 ga watan Yuli ne aka samu gawansu cikin wata motar makwabcinsu, inda ake tsammanin zafi a rashin isak ya kashe yara 3 daga cikinsu.
KU KARANTA: Daki daki: Yadda Buhari ya fara rashin lafiyar a bana
Yaran sun hada da Aisha Sulaiman Hashim mai shekaru 3 da rabi, Rabiatu Aminu Hashim yar shekara 4 da rabi, sai Hamza Aminu Hashim da Abubakar Sulaiman Hashim dukkaninsu masu shekaru 2 da rabi. Inda a cikinsu Rabi’atu ce kadai ta sha.
Mahaifin Abubakar da Aisha, Malam Sulaiman Hashim ya bayyana cewar “Yayin da aka fara cigiyar neman yaran, sai da mahaifiyata ta leka cikin wannan motar dake fake a gidan makwabcinmu, amma bata ga komai ba.
“Kwatsam sai gashi an kawo mana labarin an tsinci gawawwakin yaran a cikin motar a ranar Asabar, inda aka same su tsirara alhalin sun fita daga gida suna sanye da kaya a jikinsu. Wannan yasa muke tunanin kashe su aka yi.”
Yaran kamar yadda Sulaiman ya bayyana, yayan wad a kan kani ne, biyu daga cikinsu, Aisha da Abubakar yayan Sulaiman ne, sai dayan su Hamza yaron yayan Sulaiman ne, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Kaakakin yansandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo yace suna gudanar da bincike don gano yadda aka haihu a ragaya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Kalli yadda aka salwantar da rayuwar wasu yara:
Asali: Legit.ng