Kashedin ku 'yan mata! Illoli 5 da kwalliyarr zamani ke yi wa fuska
Yanzu dai a iya cewa irin wadannan kwalliyoyin sun zama ruwan dare ga al'ummar mu musamman ma ga yan mata da kuma zawarawa, kai a wani lokacin ma harda matan aure.
Abun ya bunkasa sosai a kasar Hausa don a yanzu ma har masu sana'ar ke akwai wadan da su aikin su kenan.
Wadannan irin mutane akan kira su ko kuma aje a wurin su musamman ma idan za'ayi biki ko wani shagali.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin illolin da wannan kwalliyoyin suke sawa a fuskar dan adam daga majiyar mu ta Premium Times Hausa.
1. Wasu masana sun bayyana cewa yawan yin kwalliyar nan ta zamani da ta wuce misali kan haka mace daukar ciki bayan tayi aure.
2. Haka ma dai bincike ya nuna yin kwalliyar na kawo kwararrabewar fuska.
3. Haka ma bincike ya nuna cewa wasu daga cikin sinadaran da ake anfani da su kan sa cutar nan ta Kansa.
4. Ance kwalliyar na jaza matsanancin ciwon kai.
5. Haka ma dai an bayyana kwalliyar cewa takan sa tsigewar gashin jiki.
Asali: Legit.ng