Rivas ce za ta kasance babban birnin kasa Biyafara - Nnamdi Kanu
- Shugaba ‘yan fafutukar neman ‘yancin Biyafara Nnamdi Kanu ya tabbatar da cewa jihar Rivas ce za ta kasance babban birnin kasar Biyafara
- Kanu y ace caashi-fadi ne kawai mutane suke yi na cewa jihar Rivas ba ta daga cikin yankin Biyafara
Wani Sarkin gargajiya a jihar Rivas da yake bayani ga magoya bayan Kanu, cewa duk wanda yake ikirarin cewa Jihar Rivas ba ta daga cikin yankin kasar Biyafara, ya cancanci hukunci na musamman.
Dubban mutane ne suka yi cecerundo wajen tarar shugaban masu fafutukar neman ‘yancin Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu, a potakol ranar Jumma’a 21-yuli-2017, ya bayyana haka ne wa magoya bayansa, a lokacin da yake musu jawabi cewa Jihar Rivas ce za ta kasance babban birnin Kasar Biyafara.
Kanu ya bayyana haka ne ta bakin sarkin gargajiya a lokacin da yake bayani wa magoya bayan shugaba Kanu, a layin Obigbo da ke potakol, ya ce yanzu ba gudu ba ja da baya, kuma jihar Rivas ce za ta zama babban Birnin kasar Biyafara.
Kanu ya ce ba adalci ba ne, idan har ana cire jihar Rivas Biyafara, da kuma wadanda suke cewa kabilar Ibo sun fake wa da dukiyar da ke jihar ne ba su son Rabuwa da su ba.
Sarkin ya kara da cewa” shugaban ya tabbatar da cewa babu wanda za taba musu dukiyar kasarsu, duk wanda tyake kokarin yada iri wadannan labaran kanzon kurege idan aka kama shi, sai an hukunta shi sosai.
Kamfanin dillancin labarai na Legit.ng ta rahoto cewa dubban mutane magoya bayan Kanu, sama da miliyan uku 3 ne suka je tararsa a potakol a ranar Jumma’a 21-yuli-2017.
Yayin da yake bayani wa magoya bayansa “ ya ce zancen da ake yin a Najeriya kasa daya ce ba ta taso ba, muna kan bakanmu na fafutukar neman ‘yancin kai har sai mun tabbatar da kasar iyafara. Ba gudu ba ja da baya”.
don samun labarai masu dadi da kayatarwa ku ziyarce mu a shafukan sa da zumunta
https://business.facebook.com/naijcomhausa/#
email@ labaranhausa@corp.legit.ng
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng