Kotun koli ta ruguza APC sak a Kano, ta nada dan PDP a matsayin dan majalisa

Kotun koli ta ruguza APC sak a Kano, ta nada dan PDP a matsayin dan majalisa

Siyasar nan ta APC sak tazo karshe a jihar Kano bayan da kotun koli ta soke zaben wani dan majalisa a jihar ta Kano dan APC ta kuma maye gurbin sa da na jam'iyyar adawa ta PDP.

Kotun ta Allah-ya-isa ta soke zaben dan majalisar da yake wakiltar kananan hukumomin Kura da Garum malam Hayatu Dorawar-Sallau,tare da bada umurnin maye gurbinsa da dan takarar jam'iyyar PDP, Abdullahi Mohammed wanda yazo na Biyu a zaben 2015.

Kotun koli ta ruguza APC sak a Kano, ta nada dan PDP a matsayin dan majalisa
Kotun koli ta ruguza APC sak a Kano, ta nada dan PDP a matsayin dan majalisa

Legit.ng ta samu labarin cewa tun farko dai wani dan jam'iyyar ta APC be mai suna Danlami Karfi wanda yayi takarar zaben share fage tare da Hayatu Dorawa yana kalubalantar yadda jam'iyyar ta APC ta gudanar da zaben.

Bayan da akayi ta tafka shari'a wadda har ta kai su ga zuwa kotun koli, a nan ne sai kotun ta bayar da umurnin su duka sun rasa kujerar sannan kuma tace a ba dan takarar jam'iyyar PDP satifikete din shaidar cin zaben .

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng