CBN: A bara, Naira biliyan 12 jama'ar Najeriya suka rasa a damfarar ire-iren su MMM

CBN: A bara, Naira biliyan 12 jama'ar Najeriya suka rasa a damfarar ire-iren su MMM

- An so a hana jama'a shiga tsarin ninka kudinka amma sunka ki ji

- An washe da yawa da suka zuba kudinsu a tsarin MMM

- Har yanzu ba'a sake jin duriyar su ba

Babban bankin kasa, wato CBN yayi gargadi ga 'yan Najeriya da su guji shiga harkar kasuwancin da bashi da cikakken tsari, da kariya. Kuma ya bayyana cewa masu saka hannun jari a irin wannan tsari sunyi asarar kimanin naira N11.9 na biliyan a disambar bara.

CBN: A bara, Naira biliyan 12 jama'ar Najeriya suka rasa a damfarar ire-iren su MMM
CBN: A bara, Naira biliyan 12 jama'ar Najeriya suka rasa a damfarar ire-iren su MMM

Mukadashin shugaban sashen mu'amala da cibiyoyi na babban bankin (Cooperate Communication Department na CBN din), Mista Isaac Okafor ya fada, a taron kwanaki biyu na wayarwa bisa mayar da hankali matuka kan harkoki kasuwanci ga bankuna, da CBN ta kaddamar, a jiya a Kano.

Taron wanda ya sami wakilci daga malam Yusuf Wali yace babban bankin, tun 2015 yake ilmantar da 'yan Najeriya a kan harkokin bankin dan wayar masu da kai kan irin wadannan bankunan bogi.

"Manufofinmu na da sauki. Muna son ku fahimci irin aikin mu a babban bankin. Muna so mu jawo hankali ku ga hakin da ke kanku a matsayin u na 'yan kasa dan kare darajan Naira da kuma wasu harkokin na daban." a cewar Jami'in, Mista Okafor.

DUBA WANNAN: Rahoto: A 2016, Najeriya ce tazo ta daya a ta'addanci

Ya kara da cewa, babban bankin na CBN, ya fitar da tsare tsare don taimakawa tattalin arziki da zai haifar da ci gaba mai dorewa. A cewar sa tsarin zai shafi fannoni daban-daban na tattali arzikin kasa.

A bayanin ta, mukadashiyan shugabancin ofishin babban banki da ke kano, malama Bilkisu Mahe Wali tayi korafin gazawar bayar da hadin kai ga babban banki da ga cibiyoyi da hukumomin da ke da alaka da bankuna.

"A dalilin haka ne ma, babban bankin ya shirya wannan tsarin wayarwa dan sanar da jam'a garabasar da babban banki ke dashi da zai amfani jama'a" A cewar Malama Bilkisun.

Ta kuma koka da cewa, rashin wayewar jama'a kan harkokin da kuma tsare tsare na babban bankin shi ya hana jama'a cin moriyar shirye shirye da tsare tsare masu amfanin gaske.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng