Barawon tukunyar farfesun nama ya gamu da fushin kotu, ya sha bulalai!

Barawon tukunyar farfesun nama ya gamu da fushin kotu, ya sha bulalai!

Wata kotu dake garin Gudu a babban birnin tarayya Abuja ya ta yanke ma wani matashi mai suna Ameh Abah hukuncin bulala 4 sakamakon satar tukunyar farfesu da yayi daga dakin wata mata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan barawon Farfesu ya gurfana gaban kuliya manta da sabo, inda ake tuhumarsa da laifin satar wata tukunya dake cike da farfesu a daga na’urar sanyaya ruwa mallakin wata mata.

KU KARANTA: Wani matashi ya kwashi kashinsa a hannu daga sakamakon jarabawar WAEC

Ita dai wannan mata da aka sace ma Tukunyar Farfesu mai suna Uwargida Eneh Aboje tana da wani shagon ne na cin abinci, ta kai karar Abah ne ofishin Yansanda dake Durumi a ranar 15 ga watan Yuli.

Barawon tukunyar farfesun nama ya gamu da fushin kotu, ya sha bulalai!
Farfesu

Dansanda mai kara Felix Ogbobe ya shaida ma kotu cewa uwargida Ene tayi ikirarin cewa tukunyar tata da aka sace na cike ne da farfesun nama da kifi, wanda kudinsa ya kai N25,000.

Sai dai tuni Abah barawon farfesu ya amsa laifinsa, kuma ya nemi sassauci daga hukuncin kotu, nan da nan shi kuwa alkali ya bada umarnin a yi masa bulala hudu na kashedi, sa’annan ya biya matar kudin farfesun ta.

Bugu da kari mai shari’a Umar Kagarko ya umarce shi daya share farfajiyar kotun daga farko har karshe, tsaf tsaf, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Menen bukatar maza a soyayya?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng