Iran ke tallafawa 'yan ta'adda a Duniya da kudade, inji Amurka
- Iran na aika makamai da kudade ga 'yan tawayen kasashe inji Amurka
- A Najeriya ma dai an taba kama makamai daga Iran
- An kame shugaban 'yan Shi'a na Najeriya tun a 2015
Ma'aikatar wajen Amurka ta fidda rahoton shekara-shekara kan ta'addanci a duniya, inda ta ayyana kasar Iran a matsayin kasa da har yanzu take taimakawa wasu masu ta'addanci da kudade da makamai.
Rahoyton ya ayyana kasar Iran a matsayin kasar Islama da ke taimakawa Falastinawa da 'yan kungiyar Hizbulla.
A kasar Yemen ma dai, wasu 'yan tawaye sun kori shugaban kasar da saka hannun kasar Iran, haka ma a Lebanon, kungiyar Hisbolla ta fi gwamnatin kasar ma karfi.
A kasar Najeriya ma, kungiyar 'yan uwa Musulmi na samun kudade daga Iran, kuma gwamnati tayi zargin cewa suna shiri ne na kawar da gwamnati domin kafa tasu mai biyayya ga kasar Iran.
DUBA WANNAN: 2019: Buhari ne zai lashe zaben idan anyi
Iran de Mazhabar shi'a take bi, haka ma kungiyar Hizbullah. Gwamnatin Obama dai ta fara farfado da dagantaka tsakanin Iran da Amurkar, sai kuma a yanzu shugaba DOnald Trump yayi fatali da wannan shiri.
Kasar Iran dai ta nuna sha'awarta na kokarin samun makamashin na nukiliya, da iya harba makamai masu linzami, wanda hakan inji Amurka da kawayenta, kokari ne na a kori yahudawa daga yankin.
A 2016, Amurka ta wallafa wani rohoton irin wannan, wanda ke nuna kungiyoyi irin su IS, alqaeda, da Taliban a matsayin wadanda suka yi fice wajen ta'addanci a duniya. Sai dai rahotan baya nuna alakar Iran da wadannan kungiyoyi na wahabiyanci.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng