Wani mutum ya kashe 'yar shi mai shekaru 17 saboda tana soyayya da musulmi

Wani mutum ya kashe 'yar shi mai shekaru 17 saboda tana soyayya da musulmi

- Ana zargin wani mutum da kashe 'yar shi saboda tana soyayya da wani musulmi

- Ana zargin shi saboda 'yar ta shi ta ki barin wannan saurayi

- Wannan mutum dai yace ba shi ya kashe wannan 'ya ta shi ba

Ana zargin wani mutum kirista mai shekaru 58, Sami, da kisan 'yar shi me shekaru 17, a garin Ramle dake kasar Izra'ila.

A ranar talata 13 ga watan Yuni ne, aka samu gawar wannan budurwa mai suna Henriette Karra, a dakin girkin gidan na su, da yanka na wuka kala-kala a wuyanta.

Rahotanni daga MAIL ONLINE, sun bayyana cewa, an kama wannan mutumin da matarsa da kuma wani dan uwan shi da suke zama tare a gida daya da wannan budurwa, don ana zarginsu da hadin kai wajen kashe ta.

Wani mutum ya kashe 'yar shi mai shekaru 17 saboda tana soyayya da musulmi
Wani mutum ya kashe 'yar shi mai shekaru 17 saboda tana soyayya da musulmi

Ana zargin wannan mutum da kashe 'yar ta shi saboda soyayya da take da wani saurayinta musulmi, wanda mahaifin na ta ya yi matukar nuna rashin yarda da shi saboda kasancewar shi musulmi.

Dalilin soyayya da wannan saurayin ne, wani lokacin mahaifin na ta yake mata dukan tsiya har ma zaburar da ita da yake yi akan cewa sai ya kashe ta idan har ba ta bar soyayya da wannan saurayi ba.

A makonnin da suka gabata kafin ta rasa ran nata, ta aikawa kawayenta sakonni ta wayar sadarwa, wanda ta bayyana musu irin kalubalen da take fuskanta a gidansu, don mahaifanta sun ce sai sun ga bayanta saboda wannan soyayya da take da musulmi.

KU KARANTA: An dakatar da sayar da kadarar abokin Diezani a Amurka

An samu rahoto a daren da aka kashe ta daga makotan su, cewa, sunji mahaifin na ta yana ikirari da sai ya kashe ta sun huta, gwara a su yada ta kamar kare don ba ta da amfani a wajensu.

Daga wata majiya kuma, ashe 'yan sanda sun dasa na'urorin daukan sauti a cikin gidan, ta dalilin wannan sakon da ta aikawa kawayenta na kalubalen da take fuskanta.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na facebook ko twitter a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng