Anyi gumurzu a kofar shiga Masallacin Ƙudus tsakanin Sojoji da Musulmai (HOTUNA)

Anyi gumurzu a kofar shiga Masallacin Ƙudus tsakanin Sojoji da Musulmai (HOTUNA)

Rikici tsakanin yahudawa da Falasdinawa na cigaba da kamari, inda a satin data gabata ya dauki sabon salo bayan fitar da wasu sabbin sharudda da hukumomin kasar Isra’ila suka gindaya ma Musulmai.

Legit.ng ta ruwaito, hukumar Sojin kasar Isra’ila ta fito da sabbin dokoki da suke bukatar Musulmai su tsare kafin su shiga Masallacin, da suka hada da amfani da na’aurar bincike akan su.

KU KARANTA: Boko Haram: rundunar Soji ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da Jami’ar Maiduguri

Sai dai hakan bai yi ma musulman kasar dadi ba, inda suka ki amincewa da dokokin, sa’annan suka yanke shawarar gudanar da sallolinsu a wajen Masallacin, kamar yadda suka yi a ranar juma’an data gabata.

Anyi gumurzu a kofar shiga Masallacin Ƙudus tsakanin Sojoji da Musulmai (HOTUNA)
Masallacin Ƙudus

Babban limamin Masallacin, Omar Al Kiswani yace wannan dokokin da aka gindaya ma musulmai cin zarafi ne kawai, don haka ba zasu amince da su ba, sa’annan ba zasu zura idanu su kwace Masallacin ba.

Anyi gumurzu a kofar shiga Masallacin Ƙudus tsakanin Sojoji da Musulmai (HOTUNA)
Masallata a Masallacin Ƙudus

Ko a satin data gabata sai da Sojojin isra’ila suka rufe Masallacin gabaki daya. Wannan shine karo na biyu cikin shekru 48 da aka taba rufe Masallacin a irin wannan yanayi.

Anyi gumurzu a kofar shiga Masallacin Ƙudus tsakanin Sojoji da Musulmai (HOTUNA)
Masallata a Masallacin Ƙudus

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Yaron wani Fasto ya Musulunta:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng