Wasu manyan yan Boko Haram sunyi saranda (Hotuna)

Wasu manyan yan Boko Haram sunyi saranda (Hotuna)

-Muna kira da sauran mayakan Boko Haram da suyi koyi da wanda ke ajiye makamansu

-Duk wanda sukayi saranda da kansu zasu samu kullawa mai kyau

Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya, Brigadier Janar Sani Usman ya bada sanarwa ta shafin rundunar dake facebook cewa a ranar litinin 17 ga watan Yuli,cewa wasu manyan mayakan Boko Haram guda hudu sun fito daga wurin da suke buya kuma sunyi saranda a sansanon Bataliyan soji na 120 da ke Goniri.

Wasu manyan yan Boko Haram sunyi saranda
Wasu manyan yan Boko Haram sunyi saranda

A cikin mayakan Boko Haram din da sukayi surrender har da Konto Fanami, wanda shine shugaban yan Boko Haram da ke buya a garin Kafa inda suke aikata ta’adancin su a hanyan Ajigin zuwa Talala da Mungusum.

KUMA KU DUBA: Hannun karba hannun mayarwa a 2019 - Goodluck Jonathan

A lokacin da jami’an sojin ke musu tambayoyi, sun ce sun fito ne daga wurin buyansu kuma sun ajiye makamai saboda tsananin wahala da suke fuskanta kuma har ila yau sun gane cewa shugabanin su rude su kuma sun daura sun kan bata.

Mayakan da sukayi sarandar sunyi nadaman barnar da sukayi kuma sunyi mamakin irin kullawa mai kyau da jami’an sojojin da suka karbe su suka karbe su basu.

Muna kira ga sauran yan Boko Haram da suyi koyi da wadannan, su tuba kuma su ajiye makaman. Duk wanda sukayai saranda da kansu za’a basu kulla mai kyau.” Inji Brig. Gen Usman

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng