Yadda ɗan Boko Haram ya lahanta wani yaro a daren da suka sace yan matan Chibok
Wasu hotunan ban tausayi sun bayyana na wani yaro wanda wani dan Boko Haram yabi ta kansa da babur a daren da yan Boko Haram din suka sace yan matan Chibok.
Wannan yaro da jafa’in nan ya afka masa sunansa Ali Ahmadu, kuma shekarunsa 6, a daren da yan Boko Haram suka saci matan Chibok ne daya daga cikin yan ta’addan ya bi ta bayan Ali Ahmadu akan Babur, wanda hakan yayi sanadiyyar balla masa kashin baya.
KU KARANTA: Shekaru Uku kenan da na raba jaha da Nafisa Abdullahi a soyayya – A Zango
Legit.ng ta ruwaito wani ma’abocin shafukan Facebook George Onmonya Daniel ya bayyana wannan labari a shafinsa, inda yace a jiya ne wani bawan Allag Nuhu Fulani Kwajafa ya kawo shi garin Abuja, don garzayawa dashi kasar waje inda ake sa ran bashi kulawa na musamman.
Tun bayan da wannan lamari ya wakana, Ali bai sake taka kafarsa ko motsawa ba, har sai yanzu da wata kungiya mai zaman kanta ta taimaka masa da yunkurin kais hi kasar wajen domin samun kulawa.
Ana bukatar jama’a da’a taimaka ma Ali Ahmadu ta hanyar aikawa da kudi zuwa asusun kudi na bankin Eco, mai suna Global initiative for peace, love and care. Da lambar asusu: 3362017526. Ko a samu Nuhu Kwajafa akan lambar waya: 0816 318 3797.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Yadda Sojoji suke ragargazan yan Boko Haram:
Asali: Legit.ng