Kungiyar lura da hakkokin musulmai Maiwa da CAN Martani akan koyarda IRK da CRK
Kungiyar lura da hakkin musulmai da aka sani da (Muslim Rights Concern, MURIC),ta bada jawabi a ranar litinin inda tayi watsi da surutai da yawo da jitajitar cewa ana neman Musuluntar da kasar Nageriya.
A jawaban Shugaban kungiyar ta MURIC, Ishaq Akintola Legit.ng ta nuna yayi Allah wadai da jitajitar jama'an tareda nuna cewa basuda dalili gamsah-she.
MURIC na nufatar wannan zancen ne musamman da kugiyar dattijan kiristocin Christian Elders Forum, NCEF a surutansu na nuna cewa anason musuluntar da kasar.
Jagororin Kungiyar ta NCEF da ta kunshi tsofarfin janar janar na sojoji su nemi a sake waiwayawa tared sabanta tsarin ilimantar da addini a kudin karatun kasar baki daya
A wani martanin da MURIC tayi musu ta nuna cewa hakan yunkuri ne na mukabalantar musulman kasa tareda nuna kyamatarsu da adawa wa addinin. MURIC ta kara nuna cewa ruwa ne ya karewa yar kada wato NCEF dake ribatar addinanci gun haddasa fitina tsakanin 'yayan musulman mazauna yankunan da suke hari do yada addininsu
Menene laifin mayarda darasin addinin Islamiyyah dole wa musulmai, da kuma kiristanci wa kiristoci? shin wannan ma na daga cikin yunkurin Musuluntar da kasar Njeriya? MURIC ta aika musu da tambayoyin.
KU KARANTA: Ruwan sama: Jama'a na cikin hadari a Najeriya - Inji Farfesa Sani Mashi
A wasu Rahotannin da Legit.ng ta samo, akwai yunkurin zagon kasa ga maluman Islamiyyah IRK da kungiyar CAN keyi don ganin musulmai basu cinma burinsu ba.
Daga cikin gurare akwai inda ake hana koyar da IRK ta hanyar tilasta maluma da koyarda wasu madojin a maimakon IRK, idan kuma suka ki ana musu barazanar kora a yayinda kuma ta daya bangaren nan take ake bawa wadanda suka karanci addinin CRK aiki.
MURIC ta nuna cewa dukkanin bayanan da muka gabatar nada dalilai masu karfi da zasu karfafesu, kuma mun kaddamar da jawaban mu na kai kara wa hukumar ilimin kasa baki daya.
MURIC, ta nemi hukumar sojojin Najeriya dasu ja kunnen tsofarfin jami;oinsu masu ritaya daga kiristoci da su shiga taytayinsu.
Ku biyomu a facebook; https://www.facebook.com/naijcomhausa/
ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng