Jerry Gana bai yiwa Najeriya halarci ba
- Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello, Farfesa Ango Abdullahi sun ce tsohon Ministan labarai bai yiwa kasa Najeriya halarci ba saboda wani furuci da yayi akan rabewar kasar nan.
Tsohon ministan labarai, Farfesa Jerry Gana ba shi da halarci a cewar gwamnan jihar Kano, Ganduje, Ango Abdullahi da Dakta Junaid Muhammad.
Sun bayyana hakan ne a lokacin da suka je ta'aziyya ga iyalan marigayi Dan Masanin Kano, Maitama Sule, saboda wani furuci da tsohon ministan labarai ya yi.
Tsohon ministan ya yi bayani sanadiyar ballewar rikicin Biyafara akan sai an raba kasar nan, cewa, kudu maso tsakiyar kasar nan baza su bi Najeriya ba idan har abin ya kai da sai an raba kasar nan.
Abdullahi yace, furucin Gana ya yi muni, kuma wannan shi yake nuna irin rashin halarcin na sa, duba da irin alherin da ya samu lokacin kawunan kasar nan na hade.
KU KARANTA: APC tayi wa PDP dukan babban bargo a zaben Jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kano ya kara da cewa, Najeriya baza ta cigaba ba matukar babu hadin kai daga kowane sashe na kasar nan. Kuma wannan furuci na Farfesa Gana yayi munana domin basu ji dadin sa ba kwarai.
Sun kara da cewa, ace kamar farfesa wanda duk abinda ya zama kasar nan ce ta maida shi amma yake goyon bayan a raba ta. Sun ce lallai ya kamata a duba wannan al'amari don duk mutumin da ya kai matsayin farfesa ba zai yi wannan tabokara ba.
https://business.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng