Bincike: Shan kayan maye na haifar da ciwon tabuwar kwakwalwa a tsakanin matasa
Yawan shan giya da da sauran kayan maye na barin matasa kimanin 2,014 a kasa.
Hukumar yaki da shan kayan maye da kwayoyi na kasar Mozambique da akasani da (GPCD) sun bada kiyascin mafi yawan wadanda hakan ke cikawa dasu daga matasa sune yan shekaru tsakanin 16 zuwa 25.
Daraktan GPCD Sara Jafete ta fada a nakaltowar Legit.ng cewa "mafi yawancin yaran sun kasance yan matakin makarantar sakandare ne.
"Sau dayawa yara kan hada kwayoyin da kayan sha domin kada malumansu su gano makircin da suke kullawa, aukuwar ire-iren wadannan waki'ar yana nan birjik a asibitocn kasarmu na Maputo."
Hukumar a rahoton Legit.ng ta bada koyarwa tareda kashe makudan kudade a makarantu da dama a gurare da dama don taimakawa gurin magance ko rage wannan fitinar.
Wasu daga dalilan dakesa yara shiga harkar shaye-shayen shine batasu da wasu iyayen keyi da kudade a hannu da sunan kauna da suke musu.
KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya kai ma Shehi Dahiru Bauchi ziyara (HOTUNA)
A shekarar nan mun kama mutane 94 daga masu sayarda kwayoyin maye wa dalibai masu cutarwa wa rayuwarsu.
kwamandan yan sanda na birnin Maputo Bernardino Rafael ya sanar da cewa suna aiki tare da hukumar kut-da kut kuma sunyi nasara matuka gun karya kashin bayan harkar shaye-shaye a kasar.
Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/
Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng