Matatar man fetur na Warri, Kaduna, da PH suna samar da kalanzir lita miliyan 5 a yini -NNPC

Matatar man fetur na Warri, Kaduna, da PH suna samar da kalanzir lita miliyan 5 a yini -NNPC

Kungiyar Man fetur ta Najeriya, wato Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) a ranar Lahadi sun bada sanarwar cewa masarrafin man fetur din kasar na fotakwal,warri da kaduna suna samar da litar kalanzir miliyan biyar a yanzu haka a yini, wanda hakan ke wakiltar kaso 60 daga lita miliyan 8 dinda akebukata a yini a kasa baki daya.

A wani jawabin na NNPC a birnin tarayya na Abuja wa majalisar zartarwa, a yawun manajan yankuna Mr. Maikanti Baru,ya nuna cewa karashen lita miliyan 3 shine abinda ake sayowa daga waje, wanda yan kasuwar harkan mai keyi.

Mista Baru ya shawarci yan majalisar da su bibici kungiyoyin man fetur Musamman DRP da majibinta lamurransu don samun cikakken bayanin yanda akeyi ake shigo da kalanzir mara kyau kasar da marasa gaskiya keyi.

Matatar man fetur na Warri, Kaduna, da PH suna samar da kalanzir lita miliyan 5 a yini -NNPC
Matatar man fetur na NNPC

Legit.ng ta ruwaito cewa yayi kira ga ita kungiyar ta DRP da tayi aiki tareda hadin kan majalisar zartawa da gaskiya gurin tabbatar cewa yawan man fetur da ingancinsa da yan kasuwar man fetur ke shigowa dashi bai sabawa ka'idoji da sharuddan da NNPC ta gindaya ba don rashi yin hakan na iya jawo cikas ga cigaban kasa baki daya.

KU KARANTA: Mutane 9 sun mutu yayinda motar tankan mai ya tashi a Calabar

Ingancin kalanzir da ake sayarwa da jama'ar kasa na da bukatar a lura dashi matuka don alakarsa da cinma kyautatuwar lafiya,tsaro,da kyautatuwar muhalli a ko yaushe a rayuwar yan kasa.

Baru ya nuna cewa Kalanzir din da NNPC ke samarwa ya cika wadannan sharuddan, domin NNPC na tabbatarda dukkanin wadannan ta hanyar bibitar matatar man feturansu na kasa baki daya, kuma kungiyar a koyaushe bazata kasance mai sabawa ka'idoji da hakkokin kasa ba.

Ku biyomu a facebook; https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter; https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng