‘Yan sanda: Za a dauka karin 'yan sanda 155,000 a Najeriya

‘Yan sanda: Za a dauka karin 'yan sanda 155,000 a Najeriya

- Sufeto-Janar na 'yan sanda ya ce ana sa ran za a dauki karin jami’an ‘yan sanda 155,00

- Hukumar ‘yan sanda ta ce ta nema amincewar fadar shugaban kasa

- Idris ya ce rundunar ‘yan sanda za ta kare kowa a kowane lokaci

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta nema fadar Shugaban kasa domin ta amince karin ‘yan sanda 155.000 nan da shekaru biyar masu zuwa.

Sufeto-Janar na 'yan sanda, Alhaji Ibrahim K. Idris ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, yana mai cewa hukumar ‘yan sanda ta nema daukan karin ‘yan sanda 31.000 a kowace shekara har nan da shekaru biyar.

Idris ya lura da cewa, daukar wadannan ma'aikatan zai taimaka wa hukumar 'yan sanda wajen cimma kudurin Majalisar Dinkin Duniya a kan dan sanda daya zuwa mutane 400.

‘Yan sanda: Za a dauka karin 'yan sanda 155,000 a Najeriya
Sufeto-Janar na 'yan sanda, Alhaji Ibrahim K. Idris

Legit.ng ta ruwaito cewa, Alhaji Idris ya ce hukumar 'yan sanda ta gabatar da bukatar kafa wani asusu ga majalisar kasar ta yanda za iya magance kalubalen da hukumar ke fuskanta.

KU KARANTA: An gano masu tallafawa kungiyoyin ‘yan daba a yankin Neja Delta

Idris ya bukaci 'yan Najeriya cewa kasu yada wani rukuni na mutane su yi musu barazanar ficewa daga wani yankin kasar. Ya tabbatar cewa rundunar 'yan sandan kasar za su kare kowa a kowane lokaci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng