Ina kishingide zan sami makudan kudi ta hanyar chanji in naso - Sarkin Kano SLS II
- Sarkin Kano yayi tsokaci kan tattalin arziki
- Ya ce ya kamata jihohi suyi koyi da jihar Legas
- Yace da yawan biliniyoyi sun sami kudinsu ne ta hada-hadar chanji
A taro da aka gudanar a jiya a jihar Kano, kan tattalin arziki, wanda gwamnatin tarayya ta shirya, Sarki Sanuni yace dole ne gwamnatoci suyi koyi da yadda jihar Legas ta iya kirkiro wa kanta hanyoyin samun kudi da lamuni.
A cewar Mai-Martaba dai, basuka sunyi wa kasar nan katutu, domin duk wata kwandala da gwamnati ta samu, tana kashe kwabbai kusan 40 a kan biyan bashi, inda ya ce hakan baya iya habaka tattalin arziki.
A cewarsa, wasu na gefe suna samun makudan kudade, kawai domin suna da jari, yace ko ni ma, da yadda na fahimci harkar banki, da ina so, daga kishingide a lambu na zan iya juya naira da dala ta harkar chanji in kuma sami makudan kudade
DUBA WANNAN: Buhari ya hakura da tsayawa takara a 2019
'Ko biloniyoyi da kuka ji ana cewa sunyi kudi dare daya ta wannan hanya ne sunka sami kudadensu' inji Mai martabar.
A baya ma dai Sarki Sanusi ya kwabi gwamnatin shugaba Buhari kan yadda ta bari har Naira tayi tashin gwauron zabi a kasuwar chanji, inda ya ce mutane suna zagaye kasa da kudin waje suna samun ribar N100 kan kowacce dala daya.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng