YANZU YANZU: An kashe wata sakatariya a jihar Kogi
- Sakatariya ta fada hannun miyagu
- Ta rasa ranta ta hanyar harbi da harsashi
- ‘Yan uwa da abokan arziki sun yi rashin wannan mata
Wasu ‘yan bindiga dadi sun harbe wata sakatariya ta din-din-din ‘yar asalin jihar Osun, mai suna Mrs Olufunke Oluwakeme Kolawale a kan hanyar Okene ta jihar Kogi.
Wannan abu ya faru ne a safiyar ranar alhamis, a kan hanyar ta ta zuwa birnin tarayya, domin taya murna ga wata aminiyarta a kan samun karin girma da tayi na zama joji; a yayin da ta cika a asibitin Lokoja bayan anyi gaggawar kaita asibitin.
Wani dan’uwa ga marigayiyar, Mr Femi Ajibade, ya bayyanawa manema labarai na DAILY POST a ranar juma’a cewa; sun ji mutuwar wannan ‘yar’uwa tasu kuma wannan babban rashi ne a gare su.
Yace, tun a yammacin ranar alhamis din ne su kayi ta kokarin neman ta ta hanyar wayar sadarwa amma suka ji shiru, sai daga bisani yace bari yaje gidanta wanda yake unguwar Ofatedo yaji ko lafiya; amma da isar sa gidan ya samu labarin abinda ya faru da wannan ‘yar’uwa tasu.
KU KARANTA: Lokaci ya yi da Najeriya za ta fara fasfot na shige da fice a kasar
Sun fara shirin zuwa jihar Kogi domin ganin halin da take ciki, sai wasu abokan aikinta suka tabbatar musu da cewa ai tace ga garinsu nan sai dai kawai suyi hakuri.
DAILY POST sun kawo rahoton cewa; marigayiyar ‘yar asalin unguwar Modakeke ce, ta karamar hukumar Ife a jihar Osun kuma wannan mata tana daya daga cikin sakatarori masu fada a ji a jihar tasu da kuma kwarewa a kan aikinta.
https://business.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng