Yanzu-Yanzu! Dan majalisar Sokoto Wamakko ya rasu yau
1 - tsawon mintuna
- Dan majalisa daga Sokoto ya rasu
- Dan majalisar yana wakiltar mazabar Wamakko ne
- Dan majalisar ya mutu yau Juma'a
Labarin da ke iso mana yanzu yana nuni da cewa dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Wamakko mai suna Alhaji Abdullahi Namdas Wammako ya rasu yau din nan.
Majiyar mu dai ta ruwaito cewa Wamako ya rasu ne yau a garin Abuja bayan ya sha fama da yar gajeruwar rashin lafiya.
Legit.ng ta samu labarin cewa dan Majalisar dai ya rasu ne yana da shekara 50 a duniya kuma an ma ce ya je zaman majalisa a ranar litinin din da ta gabata.
An dai bayyana cewa tuni ma dai akayi jana'izar sa a garin nashi na Sokoto kamar yadda addini ya tanada.
Asali: Legit.ng