Sarakunan gargajiya sun samu lambar yabo daga gwamnatin jihar Kebbi

Sarakunan gargajiya sun samu lambar yabo daga gwamnatin jihar Kebbi

- Gwamna Bagudu ya yi jinjina ga sarakunan gargajiya

- Sarakunan sun tsaya kan gaskiya da rikon amana

- Sun kawo karshen rikicin Fulani a jihar

Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Bagudu ya ba da lambar yabo tare da jinjinawa sarakunan Gwandu da Argungu, da kuma masu garuruwan Aliero, Gwandu, Jega, da Mayama, sakamakon irin rawar da su ka taka wajen kawo karshen rikin Fulani da manoma a jihar.

Sarakunan gargajiya sun samu lambar yabo daga gwamnatin jihar Kebbi
Sarakunan gargajiya sun samu lambar yabo daga gwamnatin jihar Kebbi

Gwamnoni yayi wannan yabo ne a fadar tasu yace, gwamnatin shi ta yi madalla da wannan abu a lokacin da kuma yayi jawabai a kan zaben kananan hukumomi da za a yi na jihar a ranar asabar me zuwa.

KU KARANTA:Siyasa: Atiku na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP

Yace gwamnatin shi za ta cigaba da baiwa sarakunan girma da kuma kokarin biyan bukatansu wanda ya rataya a wuyan gwamnatin. Sannan yana shawartar sarakunan da su tabbatar da zaman lafiya, fuskantar juna da kuma hadin kai a wannan zaben da za a gudanar a jihar.

A fadar Lammen Augie, Alahji Adamu Augie, masu garuruwan da su ka tofa albarkacin bakunan su sun hada da: Gwandu- Alhaji Bello Mai Wurno, Aliero, Alhaji Salisu Muhammad Jega, Alhaji Arzika Sarkin Kabi Jega da kuma Maiyama,Alhaji Adamu Aliyu Maiyama, sun yi godiya ga gwamnan a kan wasu aiyuka daya aiwatar a garuruwansu kuma sun tabbatar da cewa za suyi bakin kokarin su domin a yi wannan zabe lafiya.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng