Dan kasuwa Dangote ya taimakawa Hausawa da Fulanin tsaunin Mambila da kudi Naira miliyan 50
- Dan Gote ya ba Hausa da fulani N50miliyan
- Dangote yace yana jajantawa Hausawa da fulanin Mambila
- Wannan ne karon farko da wanda ba gwamnati ba ya ba mutanen taimako
Shahararren attajirin nan dan kasuwa watau Alhaji Aliko Dangote ya ba Hausawa da kuma fulanin dake a bisa tsaunin Mambila da rikicin kabilanci ya shafa a kwanan baya gudummuwar Naira miliyan 50.
Aliko Dangote dai ya ziyarci jihar ta Taraba ne a cikin satin nan inda kuma yace ya zo ne yin ziyarar jajantawa ga Hausawa da fulanin yankin sannan kuma da ta'aziyya ga iyalan tsohon Gwamnan jihar Danbaba Suntai.
Legit.ng ta samu labarin cewa wannan ne dai karon farko da wani dan Najeriya wanda ba gwamnati ba ya fara bada taimako ga wadanda rikicin ya dai-daita a saman tsaunin na Mambila.
A kwanan baya ma dai mai karatu zai iya tuna cewa tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar jihar Kano ta tsakiya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ziyarci tsaunin da nufin kawo karshen kashe-kashen da kuma lalubo bakin zaren rikicin.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng