Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kai ziyara Mambila

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kai ziyara Mambila

- Sanata Kwankwaso ya kai ziyara jihar Taraba domin gani da ido

- A baya ma, Sanata kwankwaso ya kai irin wannan ziyara kudu

- An yi wa fulani kisan gilla ne a Mambila

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kai ziyara jihar Taraba don gani da ido kan yadda hare haren kabilanci ya tagayyara jama'ar tsaunin Mambila a jihar Taraba.

Tawagar ta Sanatan, ta jajantawa mutanen yanki, sannan ta gana da sarkin Hausawa na yankin Sardauna Dr. Shehu Audu, inda yayi kira da a zauna lafiya.

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kai ziyara Mambila
Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kai ziyara Mambila. Hoto an samo shi ne sashen Hausa na VOA da ke Amurka

A baya ma dai, irin wadannan kashe kashe a jihar Osun ta saka tsohon gwamnan tattaki har zuwa inda abun ya auku, inda yayi kiran a zauna da juna lafiya.

KARANTA KUMA: Mutane sama da 1000 ne suka tagayyara a Mambila

A jihar Taraba dai, anyi munanan hare-hare kan kauyuka da suka hada da na Hausawa da na Fulani, daga wasu yan ta'adda da ake kira Mambila Milisha.

An dai kafa dokar hana fita a yankin na Sardauna da ke jihar, kuma hukumomi sun shawo kan lamarin, amma duk da haka, dubban jama'a sun rasa muhallansu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel