Sadarwa: Kamfanin sadarwa na Etisalat ta shiga uku a Najeriya
- Kamfanin sadarwa na Etisalat zata fice daga Najeriya nan da makonin 3
- Shugaban kamfanin na Najeriya yace kokarin da suka yi na shawo kan lamarin abun yaci tura
- Ana bin kamfanin Etisalat na Najeriya bashin dala Amurka biliyan 1.2
Kamfanin sadarwa na Etisalat na kasa da kasa zai rufe kasuwancinsa a Nigeria ta fice daga kamfanonin sadarwar kasar nan da makonni uku masu zuwa.
Babban shugaban kamfanin wato Cif Executive Officer (CEO), Hatem Dowidar ya sanar da hakan a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli.
Dowidar ya ce duk masu hannun jari a kamfanin Etisalat na Nigeria daga Hadaddiyar Daular Larabawa sun bar kamfanin, ciki har da mallakar asusun gwamnati Mubadala.
Ya ci gaba da cewa sun mika sanarwar hakan ne a rubuce ga mahukuntan kasar da sauran masu hannun jari a kamfanin.
KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Olumba Olumba
Kamfanin Etisalat Najeriya ta ciwo bashin dala Amurka biliyan 1.2 daga bankunan kasar 13 wanda tun a shekarar 2013 wanda suka kasa biya har yanzu bayan shekaru hudu.
Mista Dowidar yace duk kokarin da akayi na shawo kan lamarin abun yaci tura saboda haka suka yanke shawarar ficewa daga Nigeriar
Abin tambaya a nan shine ko kamfanin Etisalat zata yi la'akarin sake zuba hannu jari a Najeriya nan gaba, Dowidar ya ce babu wata halamar haka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng