Wani dalibin koyan aikin soja ya gamu da azal

Wani dalibin koyan aikin soja ya gamu da azal

- Rai yayi halinshi

- Dalibin koyan aikin soja ya riski mutuwarsa

Wani dalibin koyon aikin soja, Saviour Enoch ya gamu da karshen sa a hannun wadansu mutane da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne.

Enoch wanda dalibin makarantar koyon aiki soja ta jihar kaduna Nigerian Defence Academy (NDA) ya mutu a ranar 8/Yuli/2017 da karfe 8:00 na dare a kan hanyar Gewgwe, karamar hukumar Ovom ta jihar Bayelsa a hannun wadanda ake zargin cewa 'yan kungiyar asire ne.

Wani dalibin koyan aikin soja ya gamu da azal
Wani dalibin koyan aikin soja ya gamu da azal

Shafin Legit.ng sun ruwaito cewa dalibin dan asalin Ovom ne wanda ya zo gida saboda hutun da aka basu na makaranta. A yayin da yake kokarin taimakon wata mata da yaji tana rusa ihu cewa wasu mutane sun yi mata kwacen jaka.

KU KARANTA: Munafukan mijina za su gane kuransu idan ya dawo - Inji Aisha Buhari

Wani mazaunin wajen me suna Bodmas Kemepadei yace sanadiyar bin wannan mutanen domin karbo jakar wannan mata ne, ashe sun yi dako suna jiran wanda zai zo. Zuwan Enoch ke da wuya suka harba masa harssashi wanda ya mika shi har lahira.

'Yan uwa da abokan arziki na wannan dalibi sun rubuto a shafin facebook suna kaico da mutuwar sa da kuma jajintawa juna akan wannan rashi da suka yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel