Wani soja ya tsaya don taimakawa masu ciki a lokacin yaki da Boko Haram
A shekaru da dama ýan Najeriya na da tunani daban daban game da sojojin su saboda a tunaninsu da dama daga cikin su mugaye ne kuma marasa tausayi.
Hakan ya sha bambam ta fannin Ebuka Celestine Nwabueze. Ya tabbatar da cewa shi din na daban ne a cikin sauran sojoji dake nan sannan kuma har yanzu mata na nan suna waka tare da yabon sa a Arewa.
An rahoto cewa Nwabueze ya taimaki mata daban daban gurin haihuwa yayinda abokan aikinsa suka mayar da hankali ga yakar ‘yan taádan Boko Haram a daji.
KU KARANTA KUMA: An cigaba: An kirkiro wayar da ba ta aiki da batiri
A cewar Ikechukwu Jude Offie, wanda ya buga labarin domin karfafa gwiwar sauran ya buga hotuna da daman a sojan tare da take:
"Aikin soja abune na zuciya. Don haka... Shi ba mai reno ko dan wasar kwaikwayo ba. Sannan kuma shi ba mahaifin wadannana yara ba... ya kasance sojan Najeriya day a shahara kan ya tsaya taimakon mata masu ciki har suka haihu a Arewa yayinda yan Boko Haram ke kai farmaki a kauyen da yake aiki. Ya sadaukar da rayuwarsa don kare matar har said a ta haihu. Matar ta so sanya ma yaran sunan sa amma saboda ya kasan Kirista kuma dan kabilar Ibo daga gabas, an sanya ma yaran ABUKAR wanda ke nufin EBUKA."
Ga yadda rubutun ya zo a kasa:
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng